
Sama da mahajjata miliyan 1.6 ne suka taru a filin Arafat da ke ƙasar Saudiyya a ranar Talata domin gudanar da tsayuwar Arafah, wadda ake kallon ta a matsayin mafi muhimmanci kuma mafi tsarki a cikin ibadar aikin Hajji.
Mahajjatan sun kwashe yini suna addu’o’i, karatun Alƙur’ani da neman gafarar Allah cikin yanayi na tawali’u da ibada.
Rahotanni sun bayyana cewa, tun daga safiyar ranar tara ga watan Zul-Hijjah ne mahajjatan suka fara isa filin Arafat daga Mina, inda suka cigaba da gudanar da ibadu har zuwa faɗuwar rana kafin su wuce Muzdalifah domin cigaba da sauran ayyukan Hajji.
Malaman addinin Musulunci sun bayyana ranar Arafah a matsayin rana mai girma da ke ɗauke da rahama da gafarar Allah ga bayinsa.
A cikin huɗubar Arafah da aka gabatar da rana, an tunatar da mahajjata muhimmancin haƙuri, adalci da tsoron Allah, tare da jaddada koyarwar Annabi Muhammad SAW game da zaman lafiya da mutunta rayuka da dukiyoyin jama’a domin samun tsira a ranar gobe ƙiyama.
