NCDC na ɗaukar matakan kariya daga Ebola – Jide Idris

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya, (NCDC), ta sanar da ƙara ƙaimi wajen sanya ido da kuma ɗaukar matakan kariya kan cutar Ebola bayan ɓullar cutar a wasu sassan nahiyar Afirka. Hukumar ta ce wannan mataki ya biyo bayan ayyana ɓarkewar cutar a matsayin barazanar lafiya ta duniya da hukumar lafiya ta duniya ta yi.

Daraktan Janar na NCDC, Jide Idris, ya bayyana cewa har yanzu ba a samu ko da mutum guda da aka tabbatar ya kamu da cutar Ebola a Najeriya ba dangane da sabon ɓarkewar cutar. Sai dai ya ce hukumar na ci gaba da sanya ido sosai musamman saboda yawaitar zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashe da kuma yiwuwar shigowar cutar cikin ƙasar.

Ya ce NCDC ta gano wasu jihohi masu haɗari da iyakoki da tashoshin shiga ƙasar domin mayar da hankali wajen aiwatar da matakan kariya. Haka kuma hukumar ta ce Najeriya na da ingantattun ɗakunan gwaje-gwaje, tawagar gaggawa da cibiyoyin kula da annoba da za su taimaka wajen daƙile duk wata barazanar ɓarkewar cutar.

Jide Idris ya ƙara da cewa ƙwarewar da Najeriya ta samu a baya wajen daƙile Ebola da sauran cututtuka ta kara wa ƙasar ƙarfin shirin tunkarar wannan barazana. Ya bayyana cewa cibiyar gudanar da ayyukan gaggawa ta ƙasa tana cikin shirin ko-ta-kwana domin tabbatar da an daƙile duk wata yiwuwar ɓullar cutar a Najeriya.

By ukarofi