Bai nuna dattaku ba – Wike ya magantu akan janye takarar Fubara karo na biyu

Spread the love

Ministan Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce janyewar gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, daga takarar gwamna a babban zaɓen 2027 ya yi daidai da yarjejeniyar sulhun da aka cimma domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Wike ya bayyana haka ne bayan duba wasu ayyukan more rayuwa a Abuja, inda ya ce tun farko an cimma matsaya cewa za a dakatar da barazanar tsige Fubara, amma shi kuma ba zai nemi wa’adi na biyu ba.

Fubara dai ya janye daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne domin zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Ribas bayan tuntuɓar iyalansa da magoya bayansa domin masalahar al’umma.

Wike ya bayyana cewa bai yi mamakin matakin ba, yana mai zargin cewa ɗaukar fom din takara tun farko ya saba da yarjejeniyar sulhun da aka cimma bayan rikicin siyasar jihar.

Haka kuma, ya bayyana ɗan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, a matsayin wanda ya dace da kujerar gwamna saboda kwarewarsa a bangaren zartarwa da majalisa.

A gefe guda, ƙungiyar Rivers Professionals ta yaba da fitowar Chinda a matsayin dan takarar APC, tana mai cewa yana da kwarewa da nagartar da za su tabbatar da shugabanci mai adalci da hada kan al’umma a jihar Rivers.

Rikicin siyasar Ribas ya samo asali ne daga saɓanin da ke tsakanin Wike da magajin nasa Fubara akan iko da tsarin siyasar jihar tun bayan hawan Fubara mulki a shekarar 2023, lamarin da ya janyo aka dakatar da Fubaran har na tsawon watanni shida.

By Babaji