
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta yi kira ga mahajjatan Nijeriya da su kasance masu haƙuri, sadaukarwa da haɗin kai yayin da suka shiga sahun miliyoyin Musulumi wajen yin Ibadar ranar Arafa.
NAHCON ta bayyana ranar Arafa a matsayin lokaci na musamman yayin aikin hajji wajen neman gafara, rahama da miƙa wuya ga Allah Maɗaukakin Sarki akan dukkan buƙatun rayuwa.
A cewarta, darussa da aka samu a aikin hajjin shekarun bayan suna taimakawa wajen aiwatar da sababbin gyare-gyaren da nufin inganta walwala da zama cikin ƙoshin lafiya ga mahajjatan Nijeriya a Saudiyya.
Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa ayyukan hajji na Nijeriya ya samu ci-gaba a ‘yan shekarun nan daga matsalolin jinkiri da ke samu wajen tashin maniyyata zuwa tashi akan lokaci.
NAHCON ta kuma tabbatar wa mahajjatan cewa za a gudanar da nazari akan ƙalubalen da aka fuskanta a aikin na bana tare da warware dukkan wata matsala da aka gano don ƙaurace mata a nan gaba.
Kazalika, ta yi fatan Allah ya karɓi dukkan ibadun waɗanda suka samu halartar aikin hajjin da kuma kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu haɗin kai.
A ƙarshe, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen gudanar da aikin hajjin cikin walwala, tana mai alƙawarin ƙara ƙaimi wajen inganta ayyukanta.
