Gwamnatin Zamfara ta bada kwangilar samar da ruwa ta Naira biliyan huɗu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada kwangilar Naira biliyan huɗu don samar da ingantaccen ruwa a faɗin babban birnin jihar.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana haka a jawabin saƙon taya murnar bikin babbar sallah ga alummar Jihar.

Lawal ya c3 Aikin zai kawo ƙarshen matsalar rashin ruwa a Gusau, babban birnin jihar ba ​​da daɗewa ba.

“Nan ba ​​da daɗewa ba, matsalar rashin ruwa za ta zamo tarihi a Gusau,” In Ji Shi.

Gwamna ya roƙi alummar jihar da su ci gaba da bin doka da kuma goyon bayan gwamnatinsa na ci gaba da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Ya kuma yi kira da a cigaba da addu’o’i don samun zaman Lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Zamfara.

Lawal ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bada muhimmanci ga ayyukan da suka shafi jin daɗin jama’a kai tsaye.

Ya nuna farin cikin sa kan kammala filin jirgin saman Gusau na ƙasa da ƙasa a lokacin mulkinsa, Yana mai nuna cewar mahajjatan jihar a wannan shekarar sun tashi zuwa Saudiyya daga filin jirgin.

“Ina matuƙar farin ciki da ganin cewa gwamnatina ta kammala aikin filin jirgin saman Gusau duk da ƙalubale da dama, kuma mahajjatan mu sun tashi zuwa Saudiyya a wannan shekarar a wannan filin jirgin,” in ji shi.

A cewarsa, filin jirgin zai bunƙasa tattalin arzikin jihar tare da samar da damarmakin aiki ga ‘yan ƙasa.

Hakazalika, Gwamna Lawal ya taya al’ummar Musulmi murna a lokacin bikin Eid-el-Adha kuma ya yi musu fatan alheri don kammala bukukuwan cikin lumana.

By ukarofi