Dambe wasar maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (5)

Spread the love

(Karshe)

Daga IBRAHIM MUHAMMAD 

(Danmadamin Birnin Magaji)

Hira da Makaɗa Dan’anace Gandi/’Yartsakkuwa tare da Malam Ahmadu Sakkwato a gidan Rediyon Rima da ke Sakkwato a shekarar 1978

Kiɗa…..Za ni gidan Alhaji Alu Layi,

Mai Gabatarwa To madallah Alhaji ɗan’anace, koda yake ka rigani hanzari, to masu saurarenmu, assalamu alaikum, barkan mu da saduwa a wannan shirin namu na daga bakin mai ita.

Watau yau kuma, Allah ya kawo mu a wannan fili tare da Alhaji Dan’anace. To idan na ce dai Alhaji Dan’anace, kusan duk masu saurarenmu sun san ko shi wane ne. Alhaji ɗan’anace dai, shahararre ne ƙwarai game da sha’anin kiɗa na kalangu a wannan nahiyar tamu ta Hausa.

To Alhaji, barka da saduwa da kai a wannan shiri na daga bakin mai ita, barka da zuwa.

ɗan’anace: Barka dai Alhaji.

Mai Gabatarwa To, kamin na ce komai, to Alhaji, shi wannan kiɗa naka ko kuma ita wannan sana’a taka ta kiɗa, shin gadon ta kayi ko ko dai ka tsire tane haka kawai?

Dan’anace: Ban tsire ba kawai, akwai dalilin da ya sani kiɗi. Abinda a mahwarin kiɗi na Anace,

Mai Gabatarwa: To, ya kuke da Anace?

ɗan’anace: Anace ubana ne,

Mai Gabatarwa: To shi ne ya haihe ka koh?

Dan’anace: A’a, ƙanen tshohuwata na,

Mai Gabatarwa: To ka zama kamar kana karen makaɗa ke nan koh?

Dan’anace: Karen makiɗa nike, sosai karen makiɗa nike, saboda makiɗin da na amshi doki nai, suna da yawa karkarar mu.

Mai Gabatarwa: Gaskiya ne, to yanzu Alhaji, kamar shekarar ka ta haihuwa ta kai nawa?

Dan’anace: Ni, to yanzu dai nayi sittin.

Mai Gabatarwa: Ka shekara sittin, a kasagga, ashe an sha ruwa?

Dan’anace: Na sha ruwa, naga mutane, sunyi kallo na, na yi kallon su,

Mai Gabatarwa: To gaskiya na, haka ko ake so,

Dan’anace: Mutane sun ganni, na gansu, kuma sun sanni, na san su,

Mai Gabatarwa: To Alhaji, yanzu kaman ka yi shekara nawa kana wannnan kiɗa naka?

Dan’anace: Ni matsayin wannan kiɗin da nike yanzu, faro shi abinda ya kawo yau, shekara hamsin ina sana’ar kiɗi ko gabas ko yamma, ko kudu ko arewa. Ko ina nik kwan ciki nai nike, amma in ina lahiya. Kai ko ba ni da lahiya akwai masu kama man su tahi su yo kiɗi ina zama na. Sai su taho su yi ta roƙon Allah ya sawwaƙe mani, suna ba ni abinda na ci.

Mai Gabatarwa: Gaskiya ne, haka ko ake so ga mutum.Watau tun kana da kamar shekara goma ka fara kiɗa?

Dan’anace: Nih hwara ba, ina biye da tsoho na da ɗankurkutu ina bugu, har nikkai fagen shi ɗunka abin kiɗi shi ba ni in kiɗi ina amsawa waƙa shi ko yana hutawa tai. Ina bada waƙa, ina amsawa kuma ina kiɗi, shi ya huta. Na yi tashe shi, kamar dai yadda nike yanzu

Mai Gabatarwa: A wannan zamanin, watau kamar kiɗan kalangu ne shi mahaifin naka ya tashi da shi?

Dan’anace: Anace, kiɗi nai yawa gare shi, akwai dai kiɗin noma, yana yi bil-haƙƙi, ba sahwai makiɗi ka tahowa ya gagare shi, su yi hira wuri guda ya gagare shi. To kiɗin noma ya kai, bayan shina kiɗin noma, to amma yana kiɗin masu gari. Amma lokacin da yaka kiɗin ga, ni ga yaran da ɗana nika iza mai, ni ba ni zuwa, sai inyi zama na,

Mai Gabatarwa To yanzu a wannan zamanin, da kake tare da shi mahaifin naka kuna kiɗa, kana iya tunawa da wata waƙa ko kuma wani kiɗi wanda ka tashi tare da shi ka ga yana yi?

ɗan’anace: Ina ko tunawa, ko ban san wani ba na san wani.

Mai Gabatarwa To daga cikin kaɗe-kaɗen da ka tarar yana yi lokacin kana yaro kana yi mai amshi, ko zaka iya taɓa mana irin wannan kaɗe-kaɗe nashi?

ɗan’anace: Eh, ina ɗan tattaɓawa koda ban ƙware ƙwarai ba,

Waƙar Anace: 

Jagora:  “Kware sai zago, ɗanja baran malan, mai sa mazaje, 

Yan amshi: ‘Na shekawa gudane, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,

Jagora: Ina muka wasa? 

Yan amshi: Mu gangara hwadama inda korau, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,  

Jagora: Na Maimuna zango,

Yan amshi: Mai sa maza rugawa gudane,  

Jagora: Mu kwan dakwado, 

Yan amshi: In munka kwan saran harda ƙwaya, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka, 

Jagora: Su bakin kura, 

Yan amshi: Mai an taho a yi wasa da ƙwaya,  

Jagora: Ku ce ma nagora,  

Yan amshi: In ba shi dambe muna ba shi kwando, ya ɗauko taki babu hulla, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,

Jagora: Kashe mana ɗanmanu,

Yan amshi: In samu bawa in ɗarme darni, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,

Jagora: Randa kag bugi ɗanmanu,

Yan amshi: Bawa anini kulla talatin, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka,

Jagora: Bawa abin kunya yayyi,

Yan amshi: Mi kai shi maida bugu inda ƙwabri, kware sai zago, ƙwaya na sani mijin Abu hauka.

Mai Gabatarwa: To madallah Alhaji, watau, shi wannan taken daka tarar kuna yi tare da tsoho a can da,

Dan’anace: Da tsoho ba,

Mai Gabatarwa: Watau wannan kamar kiɗa ne na dambe koh, wato, wani shahararren Dandambe ne a wannan zamani?

Dan’anace: Eh, yana kuma da ran shi, ɗandambe ba,

Mai Gabatarwa: ƙwaya ake kiran shi?

Dan’anace: Hauka, mijin Abu hauka,

Mai Gabatarwa: ƙwaya mutumen wane gari ne?

Dan’anace: ‘Yartsakkuwa.

Mai Gabatarwa: Can garin ku ke nan. To ita ‘yartsakkuwa cikin wacce ƙasa ce?

Dan’anace: Cikin ƙasat Gandi,

Mai Gabatarwa: To, ƙasat Gandi,

Dan’anace: Eh, Yarin Gandi, shi at uban ƙasar mu, shi muka biya, mu at talakkawa nai sosai, ko yaushe.

Mai Gabatarwa: To madallah, to Alhaji. To yanzu bari mu koma mu binciki dangatakar ka da sha’anin kiɗan dambe. Na ji dai a wannan waƙar da kayyi, tun salsala ka san kiɗan dambe, ka san shi, tunda ka tarar ana yin shi, kuma ka tashi cikin masu yin shi. To Alhaji, aƙalla za ka iya gaya mani abinda ya haɗa ka da shago kamar alal misali a sana’a ta dambe?

Dan’anace: Shi shago abinda ya gama ni da shi, ya dai iske ina kiɗin dambe, tun ba zamanin shi ba, tun bai hwara dambe ba. Ina kiɗina na dambe, ina zuwa mafara, ina zuwa ‘yarkofoji, ina zuwa Bakura, ina tahowa Dambo inda dut an kayi wasa indai ta dambe ta, to tare da ni akai sai an kirai ni na tahi. In munka gama wasan mu irin na ƙauye na buki, ko na ango, ko na aure, ko in an ka gama wasan nan irin ta ƙauye, to sai mu koma ko wasat kaka muna yi, heli-heli muna wasat kaka, to sai ya iske ni, yacce man ya zo inda nike, an aika mai goron dambe ya tahi Gandi, garin Yarin Gandi, an aika mashi da goro shi je wurin wasar dambe, amma ga shi ya biyo mani yana son mu tahi tare. Nicce mai ni ba ni zuwa, ka tashi ka tahiyyakka wurin damben ka ban zuwa wannan wasa tunda ni ba aiko man anka yi ba kuma ba goro suka ba ni ba. Tunda sahe yana nan bakin ƙohwar gidanmu har la’asar ta kama, sai Anace yacce man, koni ɗan’anace ka tashi, ka tahi ka bishi, in kun ka yo wasakku, ka dawo ka yi zamanka gida shi ko ya wuce garinsu.

Da yacce man haka nicce na yarda, niɗ ɗauko kayana nig gyara, mun ka tahi Gandi, mun ka shiga, koda munka shiga wasa inda dut ta gamuwa ta gamu, dab bakin la’asar abinda yak kai zuwa mangariba, ya shiga yayyi dambe da mutun biyu, kuma ya kashe su. To shi ya tahi dani amma banyi mai kidi ba kalangu na na sarkahe haka anka taso anka dawo masafki. Sahiya ta waye anka koma aza damben ga, kuma ya kashi mutun biyu, kuma dai ban yi kiɗinga ba, kalangu na dai a rataye ga kahwada ta ban kiɗa ba, ya kuma kashe mutun hudu. To sahiya tayyi, sai anka ce ana jiran mu kurya wurin wata wasa, munka taho kurya, zamu shiga gari sai yacce ba a shiga nan wanga garin, sai an shiga da kiɗi nai. Yacce dut ‘yan damben ga da a bayan mu, wat taho da kai ba ni ba? Nicce eh, kai na taho da ni, yacce to mi ad dalili? Su ko dambe ba su yi ba, gaka kana yi masu kiɗi, ni ka ƙi yimin, mi ad dalili? Nicce eh, kiɗi bai zo ba, amma yanzu da kacce haka, yanzu da kacce haka kiɗi ya taho. To shi a mahwarinnits tsira wannan waƙat da ta game dut duniya

Mai Gabatarwa: Watau ita wannan waƙar, watau dalilin ke nan da ka soma wannan waƙar?

Dan’anace: Nan wurin da ya tare ni yacce ba za a shiga garin ga ba sai na yi mai waƙa, rai na sai ya gashe min, Sarkin da yayi ni sai taso man waƙagga,

Mai Gabatarwa: To abinda nike so, dai-dai wannan lokacin da kayi tunanin wannan waƙar, ina son su kuma masu sauraren mu da suka ji wannan tarihin haɗuwarka da shago zuwa wannan lokacin, a kaɗa mana abinda aka soma kaɗawa dai-dai wannnan lokacin.

ɗan’anace: Tau.

Waƙar Shago ta ɗan’anace: 

Jagora: To bahago,

‘Yan amshi: Ina mazan da ka ima?

Jagora: Karo da duna ba shi da daɗi,

‘Yan amshi: Baleri ba guda da guda ba,

Jagora: Ina gidan mu zaune da sahe, ɗan-Audu ya iske ni, yacce mu zo ni Gandi dambe, mun zo ni Gandi dambe, ana kiran mu rara da hwama, yacce ɗan-anace mai buga kawu, shirya mu je ni rara dambe, kuma na ce ɗan-anace ba ni da dama, wandara ka san abinda baya da daɗi,

‘Yan amshi: Kar ka kashe mutun ka barni a kam man,

Jagora: Kada ka kashe mutun,

‘Yan amshi: Ka barni a kamman, garin ga ba ni da kowa,

Jagora: Ka san halin dogarai, na san halin su bayin sarki, suna biya suna turi na, waɗansu na dwaga ta, ko tahiya sai 

‘Yan amshi: Tahi ka yo naɗi, mu koma dambe,

Jagora: Karo da duna ba shi da daɗi,

‘Yan amshi: Baleri ba guda da guda ba,

Jagora: A gaida duna,

‘Yan amshi: Mai hana ƙarya,

Jagora: Baleri sannu,

‘Yan amshi: Mai hana ƙarya,

Jagora: In mutun yacce ba shi bauɗuwa bai kwanto,

‘Yan amshi: Bai yi arangama da ɗan sababi ba,

Jagora: Baleri sannu,

‘Yan amshi: Mai hana ƙarya,

Jagora: Waɗanda aka jira sun kawo, ko can in ka ji gardama ba su zo ba,

‘Yan amshi: Wandara in ka ji gardama ba su zo ba,

Jagora: Wandara mai bugu,

‘Yan amshi: Kama da azazza,

Jagora: Dan-audu mai hagun mai dama, in hagun ta ƙiya, 

‘Yan amshi: Ka koma dama,

Mai Gabatarwa: To, na tabbata duk mai sauraren wannan shirin, ya ji dalilin salsalar shaƙuwar, saduwar Alhaji Dan’anace da shi da shaƙiƙin na shi, abokin shi, shago. Kuma kun ji irin yadda aka soma ta har zuwa ga wannan lokaci da ake ciki na wannan zamani.

To Alhaji Dan’anace, wato daga wannan lokaci, sha’anin ka da na shago, ya riga ya bayyana a duk duniya kowa ya sanku?

Dan’anace: Anka san shi, anka sanni, anka ji shi, anka ji ni,

Mai Gabatarwa: Wato dalilin shi, dalilin ka, dalilin ka, dalilin shi?

Dan’anace: Eh, sai munka taho bisa hanya munka yi kabra kowa ya hita. Da munka yi karo shi suna nai ya hita, ni nau ya hita. Dauri ina can karkarammu zama na, shi kuma yana can karkararrsu zama nai yana ‘yan buge-buge nai, ni kuma ina yan kiɗe-kiɗe na, sai Allah ya sa hanya ta kawo shi niko hanya ta kawo ni sai mun ka yi karo haka, suna nai ya hita nau ya hita.

Ko ya mutu, in nit shiga ga gari sai ance shago, niko ko na mutu in ya shiga ga gari sai ance shago ya shigo garin ga ɗan’anace dai ab bamu gani ba.

Mai Gabatarwa: Ashe ko da sauran tahiya ke nan?

Dan’anace: In Allah ya so.

Mai Gabatarwa: To madallah. To Alhaji, da yake kana ɗaya daga cikin mashahuran makaɗa namu a wannan ƙasa ta mu, na tabbata ka halarci bukukuwa da dama, shagulgula da dama da aka yi, ko kuma wasu abubuwa da suka gudana har aka gayyace ka, za ka iya tunawa da wani biki ko kuma wani sha’ani wanda aka yi wanda ya ƙayatar da kai, har kai kan ka kayyi tunanin rera wata waƙa wadda kake ganin ta yi maka daɗi a wannan lokacin?

ɗan’anace: Bukukuwa suna da dama, da dama, da dama waɗanda anka yi da ni. Dana sarakuna, naɗin sarakuna kuma da addu’ar suna wadda aka yi, suna da yawa.

Mai Gabatarwa: To shi ne nike son ka tuna da guda ɗaya ko don alherin da anka yi maka, ko kuma saboda abinda kagga an yi maka ka ji daɗin shi a zuciyar ka, shi yassa ka ƙirƙiro wannan waƙar, to ina son a buga man ita wannan waƙar in ji,

Dan’anace: To sai in hwara daga nan baki, baki. Nan  gida zan hwara wa.

Waƙar Haihuwar Mamman Tukur:

Jagora: Ni dai zuwa murna ni kai, 

‘Yan amshi: Da haihuwar Mamman Tukur,

Jagora: Ni dai zuwa murna mu kai,

‘Yan amshi: Da haihuwar Mamman Tukur, sahiyar murna mu kai,

Jagora: Gidan Alhaji Alu Layi,

‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu Layi,

Jagora: Yau fa gidan Alhaji Alu Layi ni kai,

‘Yan amshi: Yau fa gidan Alhaji Alu Layi mu ke, sahiyar murna mu kai, da haihuwar Mamman Tukur,

Jagora: Gidan Alu Layi niz zo,

‘Yan amshi: Wanga nan buki ya kasura,

Jagora: Gidan Alu Layi niz zo,

‘Yan amshi: Wanga nan buki ya ƙasura, sahiyar murna mu kai, da haihuwar Mamman Tukur,

Jagora: Nagode ma arzikin Mamman,

‘Yan amshi: Nagode ma arzikin Mamman Tukur, sahiyar murna mu kai, da haihuwar Mamman Tukur,

Jagora: Jikan hajiya Mamman Tukur kuma,

‘Yan amshi: ɗan hajiya Mamman Tukur, sahiyar murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur

Jagora: Masu roƙo kun jiya, abinda dut muka roƙo,

‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu baiwa ya kai,

Jagora: Abinda dut ni roƙa,

‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu baiwa ya kai,

Jagora: In ina bidat riga,

‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu bai wa ya kai.

Jagora: In ina bidat wando,

‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu bai wa ya kai.

Jagora: In ina bidat shadda,

‘Yan amshi: Gidan Alhaji Alu bai wa ya kai.

Jagora: Alhaji Alu Layi,

‘Yan amshi: To shi yaka bada kuɗi zai yawa

Jagora: Alhaji Alu Layi,

‘Yan amshi: Alu shi ka bada kuɗi mai yawa,

Jagora: Na taho gidan Layi roƙo, 

‘Yan amshi: ɗan-anace har ni hirgita, sahiyar murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur,

Jagora: Gidan Alhaji Alu Layi,

‘Yan amshi: Yau hwa gidan Alhaji Alu Layi mu kai, sahiyar murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur

Jagora: Na ji masu roƙon baki sun faɗi, sun ce nan Alhaji Alu Layi yake,

‘Yan amshi: Sahiyar Murna ni kai, da haihuwar Mamman Tukur,

Jagora: Ni dai tahiya murna ni kai,

‘Yan amshi: Mamman na tcahe na gode maka,

Jagora: Mamman na tcahe na gode maka,

‘Yan amshi: Mamman na tcahe na gode maka,

Jagora: Muhammadu na tcahe nagode ma,

‘Yan amshi: Allah ya tabbata mai yawa,

Mai Gabatarwa: To madallah, nima sai ince Allah ya raya. Watau wani biki ne aka yi wanda ya ƙayatar da kai kwarai da gaske? 

ɗan’anace: Nan gidan Alhaji Alu ba, na je wurin Allah shi raya,

da anka yi man kyauta, to ni, ba don ance man ka tashi ba kuma ba a sallameni ba, don kai na nij ji kumyani gudu.

Mai Gabatarwa Tirƙashi.

Dan’anace: Ni nig gudu dut da yara na nan nib bassu sai daga baya anka ce ai ɗan’anace ya tahi, in kuna tashi ku tashi.

Mai Gabatarwa: Gaskiya ne, to madallah. To yanzu kuma bari mu sake shiga cikin matsalar nan taka  ta sha’anin kaɗe-kaɗe. Domin na tabbata kai a naka ra’ayi kuma da jama’a su kan su masu sauraren kiɗan ka, na tabbata ka san wani kiɗa wanda kai kake jin daɗin shikuma idan ka kaɗa shi a gaban kowa yana jin daɗin wannan kiɗin, kana iya tunane da irin wannan kiɗin wanda kake ganin in ka buga shi kowa yana sha’awar sauraren shi?

Dan’anace: To ina iya tuna shi. Ku yara na ku zabar man wanda duk kusa so, ku sara kirya tai inbi ku.

Mai Gabatarwa To bismillah.

Waƙar Alh Sani Kangiwa:

Jagora: Ni dai Alhaji sai Kangiwa,

‘Yan amshi: Alhaji Sani Kangiwa, Yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Ni dai Alhaji sai Kangiwa

‘Yan amshi: Ni dai Alhaji sai Kangiwa, Yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Sani ɗan Turaki na Argungu,

‘Yan amshi: Baba ban rena ma ba,

Jagora: Sani ɗan Turaki na Argungu,

‘Yan amshi: Baba ban rena ma ba, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Gwamna Shehu mun gode,

‘Yan amshi: Allah yana son mutanen Kangiwa, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Gwamna Shehu mun gode,

‘Yan amshi: Allah ya son mutanen Kangiwa, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Ya yi man halin girma,

‘Yan amshi: Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Haba waɗansu maza, ba mazan kashe kumya ne ba,

‘Yan amshi: Kuma waɗansu maza, ba mazan kashe kumya na ba,

Jagora: Sani in dan duniya,

‘Yan amshi: Sani kar ka ɗau renin kowa, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Indan zaman duniya,

‘Yan amshi: Sani kar ka ɗau renin kowa,

Jagora: Ga hankuri da mutane,

‘Yan amshi: Shina garai Mamman Sani, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Allah bar mani Sani Kangiwa,

‘Yan amshi: Allah bar mani Sani Kangiwa, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Ai shekarar Allah ni dai, saboda na zo Kangiwa, Salifu mun gode,

‘Yan amshi: Alhaji Salifu ban rena ma ba,

Jagora: Salifu nagode,

‘Yan amshi: ɗan’anace bai rena ma ba, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Ana ta taro Kangiwa,

‘Yan amshi: Dan’anace ni dai ban zo ba, ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa,

Jagora: Allah Wahidun ka mai san,

‘Yan amshi: Allah Wahidun ka mai san Kangiwa, In ga mutanen Kangiwa, Mu samu albarkar juna, 

Jagora: Ni dai in ga mutanen Kangiwa,

‘Yan amshi: Mu samu albarkar juna,  yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa

Jagora: Kai ko ruwan ilmi ne, 

‘Yan amshi: Suna ga Sani Kangiwa, Ya yi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa

Jagora: Ruwan wahayi,

‘Yan amshi: Naga rijiyar ga ta Kangiwa, Yayi man halin girma, Alhaji Sani Kangiwa

Jagora: Allah ka koro Sani Kangiwa,

‘Yan amshi: Yanzu ina samun kuɗi,

Jagora: Ya yi man doki, Ya koma ya yi man Doki,

‘Yan amshi: Ya yi man mota ya bai

Mai Gabatarwa: To madallah, na ɗan abin nan naka, na katse hanzari koh? To da yake lokacin namu kurarre ne Alhaji, na san kana kaɗe-kaɗe da dama iri-iri, irin su kiɗan noma da sauran makamantan su, to Alhaji ko zaka ruhe man wannan hili da wani kiɗa na noma wanda kake jin daɗi kuma masu saurare suke sha’awa? To bismillah,

Hirar Malan Ango Zariya na gida talabijin na RKTVK da ɗan’anace wadda aka ɗauka ranar 03/09/1972

Mai Tambaya: Da muka taɓa taken shago, ba mu kai kan inda kake cewa, wai in yana biyar ta kiɗinka,

DAN’ANACE: Eh, ina halaka shi, sai na sa shi inda ba shi hitowa, sai dai mu rage kidin, mu safsafta mai kada shi haukace baki ɗai,

MAI TAMBAYA: Na’am, duk ba mu kai nan ba a waƙar, ashe mun bar waƙa da yawa?

DAN’ANACE: Eh, to mun ɗan raga,

MAI TAMBAYA: Don dai muna son mu ɗan taɓa, kuma ban tambaye ka tun yaushe ka fara waƙa ba?

DAN’ANACE: Eh, na daɗe ina kiɗi ranka ya daɗe,

MAI TAMBAYA: Ya yi kaman shekara nawa?

DAN’ANACE: Yanzu na yi kamar shekara arba’in ina yawon duniya, ko ina da ina, marabi na da hitowa dag gida ba,

MAI TAMBAYA: Shi kiɗin ka gade shi ne?

DANANACE: Kiɗi! na gade shi,

Mi as suna na?

MAI TAMBAYA:

Dan’anace,

DAN’ANACE: To Dan’anace, to Anacen, shi a ubana, shi a makaɗan garinmu,

Kuma shina nan da rai nai bai mutu ba

MAI TAMBAYA: Shi baya yin kiɗa?

DAN’ANACE: Gare shi na amshi kiɗin, shi ne ka kiɗin ‘yan dambe da, nit tashi nigga wari nai sun aje, nicce mai kai ko aje tsoho ni in canje ka,

Ai gare shi nia amshi kiɗin. Ni a canji nai, nicce gabaɗai kidi shi aje shi nid dakatad da shi gida,

Shina aka ce ma Anace.

MAI TAMBAYA: Ka yi shekara arba’in kacce kana yawatawa,

DANANACE: Ina kidin dambe, saboda kwas sanni dai, ya gane ni sai yace mini Mai kiɗin ‘yan dambe. Dan’anace ya taho, to amma babban kiɗi na, sani ab basu yi ba, ni kiɗi na gawurtacce, wanda ya ji shi ya ce na ji makiɗi, to ni kiɗi na, na noma a kidi gare ni,

MAI TAMBAYA: Na noma?

DANANACE: In mutun na son ya ji shi tsintsa tai, to wanda ya ji kiɗina na noma, to shi ya ji ni sosai,

MAI TAMBAYA: Ashe yanzu ka iya kidin noman?

DANANACE: Na ɗan taɓa shi,

MAI TAMBAYA: Yanzu in munka ce ka yi mana kiɗin noma, wa za ka taɓa, a cikin waɗanda kay yi ma waƙa na san ka yi ma wani manomi?

DANANACE: Nan wurin ba, an sani guda na yi,

MAI TAMBAYA: To ita zaka yi mana yanzun ko?

DANANACE: Yanzun ga?

MAI TAMBAYA: Wa ka yi ma waƙar?

DANANACE: Sarkin noman ƙasar mu, Garba Na-Godi,

MAI TAMBAYA: Yawwa Garba,

DANANACE: Garba Na-Godi ba

By ukarofi