Fiye da mambobin APC 40 na Majalisar Wakilai sun rasa tikitin koma wa takara a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rahotanni daga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC sun nuna cewa fiye da mambobin Majalisar Wakilai ta Tarayya 40 sun gaza samun tikitin sake tsayawa takara domin komawa Majalisar Dokoki a zaɓen 2027, lamarin da ke nuna yiwuwar samun babban sauyi a Majalisar ta gaba.

Bincike ya nuna cewa yawan sauyin mambobi a Majalisar Wakilai yana ci gaba da ƙaruwa tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, kuma sakamakon zaɓen fidda gwani na bana ya sake tabbatar da hakan.

Daga cikin fitattun ‘yan majalisar da suka rasa tikitin komawa takara akwai Hon. Nicholas Mutu daga Delta, wanda ya shafe shekaru tun daga 1999 yana Majalisar, da kuma Hon. Mike Etaba daga jihar Kuros Riba.

Haka kuma shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Prof. Julius Ihonvbere, ya gaza samun tikitin APC domin komawa Majalisar bayan ya sha kaye a hannun Andrew Ijegbia a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Jihar Edo.

A jihar Kuros Riba ma, mambobi biyar daga cikin takwas na APC sun rasa damar komawa Majalisar, yayin da wasu ‘yan majalisa daga jihohin Akwa Ibom, Riɓers, Delta, Ondo da Ogun su ma suka fadi zaɓen fidda gwani.

A Jihar Ribas kuwa, shugaban marasa rinjaye na Majalisar, Hon. Kingsley Chinda, ba zai koma Majalisar ba saboda ya karkata hankalinsa zuwa takarar gwamna.

Sai dai shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, da mataimakinsa, Hon. Benjamin Kalu, sun samu nasarar lashe tikitin komawa takara a ƙarƙashin APC.

Sauran waɗanda suka tsallake zaɓen fidda gwani sun haɗa da Betara Aliyu, Ahmed Jaha, Satomi Ahmed da wasu mambobi daga Borno da Kuros Riba.

Rahoton ya kuma bayyana cewa akwai sabbin ‘yan takara da dama da suka samu tikitin APC domin neman shiga Majalisar Wakilai karo na farko, ciki har da Hajja Fati Kakenna da Dr. Kaumi Umara Zulum.

Masana siyasa na ganin cewa wannan yawan rashin samun tikitin komawa takara daga APC kaɗai na iya ƙaruwa idan sauran jam’iyyu kamar PDP, ADC, NDC, LP da APGA suka kammala zaɓensu.

Sun kuma bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da koke-koken da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani na iya ƙara haddasa sauyi mai yawa a Majalisar Wakilai ta gaba.

By ukarofi