Atiku ya je zawarcin Amaechi bayan kada shi a zaɓen fidda-gwanin ADC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ziyara mai kama da zawarci gidan tsohon gwamnan Jihar Ribas, Cif Rotimi Amaechi, da ke Abuja bayan kammala zaɓen fidda-gwanin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, zaɓen da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kayar da shi.

Atiku ya je tare da tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, tsohon shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Ralph Nwosu, da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Ziyarar na zuwa ne bayan Atiku ya lashe zaɓen fidda-gwanin shugaban ƙasa na ADC domin tunkarar zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta bayyana sakamakon zaɓen a daren Laraba a Abuja, inda Atiku ya kayar da Rotimi Amaechi da kuma tsohon ma’aikacin banki, Mohammed Hayatu-Deen.

A sakamakon da jam’iyyar ta fitar, Atiku ya samu ƙuri’u 1,846,370, yayin da Amaechi ya samu ƙuri’u 504,117, sannan Hayatu-Deen ya samu ƙuri’u 177,120.

Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, shugabannin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Daɓid Mark, sun miƙa masa tutar takarar shugaban ƙasa ta ADC.

Jam’iyyar ADC ta gudanar da zaɓen ne ta hanyar kaɗa ƙuri’a kai tsaye bayan ‘yan takarar uku sun ƙi amincewa da tsarin tsayar da ɗan takara ta hanyar maslaha.

Da yake jawabi bayan bayyana sakamakon, Atiku ya yi kira ga duk waɗanda ba su gamsu da sakamakon ba da su haɗa kai domin ciyar da jam’iyyar gaba.

“Ina kira ga duk wanda yake jin haushin abin da ya faru da ya dawo cikin jam’iyya mu haɗa kai domin ceto dimokuraɗiyyar mu da ƙasarmu,” inji shi.

Atiku ya kuma yi kira kai tsaye ga Amaechi da Hayatu-Deen da su yi aiki tare da shi gabanin babban zaɓen 2027.

“A gare ni babu wanda ya yi nasara ko wanda ya sha kaye. Jama’a na kallonmu domin jagoranci kuma a shirye nake na jagorance su,” ya ƙara da cewa.

Sai dai duk da wannan kira, Amaechi da Hayatu-Deen sun yi watsi da sakamakon zaɓen, inda suka zargi cewa an samu kura-kurai a tsarin zaɓen.

Daga baya kuma Atiku ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai wa Amaechi a shafinsa na ɗ, inda ya ce sun tattauna matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da ke addabar Nijeriya, tare da hanyoyin da za a bi domin ceto ƙasar.

“Atiku ya ce: “Mun yi tattaunawa mai zurfi da gaskiya kan halin da ƙasarmu ke ciki, matsin tattalin arziki, rashin tsaro, da alhakin da ke kan ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa wajen neman mafita.”

Ya kuma ce ya kai ziyarar ne domin taya Amaechi murnar zagayowar ranar haihuwarsa, tare da yi masa barkwanci kan nasarar da Arsenal ta samu kwanan nan, kasancewar Amaechi babban masoyin ƙungiyar ne.

Atiku ya ƙara da cewa Amaechi ya ba shi haƙuri saboda bai samu damar shirya masa miyar Fisherman Soup ba yayin ziyarar, amma ya yi masa alƙawarin zai shirya masa ita a wata ziyara ta gaba.

By ukarofi