An jibge jami’an tsaro a Aso Rock yayin zanga-zangar su Sowore kan garkuwar makarantun Oyo da Borno

Spread the love

A yau Alhamis ne aka ƙara yawan jami’an tsaro a hanyoyin da ke yankin Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock a Abuja yayin da ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan-adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya sanar da shirin jagorantar zanga-zanga zuwa fadar.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda masu yaƙi da tarzoma sun kewaye manyan ƙofofin Aso Rock, yayin da aka takaita shiga wurin ga masu katin shaidar aiki na Fadar Shugaban Ƙasa kawai.

Sowore ya ce, shi da magoya bayansa za su gudanar da gangami daga Eagle Square zuwa Aso Rock domin matsa wa gwamnati lamba kan ceto ɗaliban makarantu da malamai da aka sace a jihohin Oyo da Borno.

Ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da kubutar da waɗanda aka sace, yana mai cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma na daga cikin manyan nauyin gwamnati.

Haka kuma, a kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta tura manyan jami’an tsaro zuwa yankunan da aka samu garkuwa da mutane, tare da ɗaukar wasu matakan ceto da ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa.

By Babaji