An kama jagoran ’yan bindiga da mataimakansa a Zamfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

’Yan sanda sun kama wani fitaccen jagoran ’yan bindiga Ali Bahago Danakulu, tare da mukarrabansa a ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.

Kakakin ’yan sanda na jihar, DSP Yazid Abubakar, ya sanar cewa an bindiga ɗaya daga cikin ’yan binrigar har lahira a yayin samamen.

Ya ce ’yan ta’addan da aka kama sun daɗe rundunar tana neman su, bisa zargin hannu a fashi da makami, ayyukan ’yan bindiga da sauran munanan laifuka a yankin.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Ali Bahago Danakulu na Kasuwan Daji da Hassan Dan Kure, shi ma mazaunin Kasuwan Daji, da kuma Dahiru Lawali na Gidan Ango.

DSP Yazid ya ce an yi nasarar kama su ne bayan bayanan sirri sahihai da suka kai jami’an tsaro kan wata gungun wasu masu aikata laifuka da ke addabar al’ummar yankin Kasuwan Daji da ƙauyukan da ke kewaye da ita.

Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin mambobi ne na wata ƙungiyar ’yan ta’adda da ake zargin Ali Bahago ne ke jagoranta, kuma sun addabi yankin..

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi gida biyar nau’ika daban-daban da sarka guda ɗaya ta ankwa, bindiga ƙirar pistol da aka ƙera a gida, babura ƙirar Boɗer guda uku da dai sauransu.

A halin yanzu, waɗanda aka kama suna tsare a hannun ’yan sanda, domin zurfafa bincike, yayin da ake ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar. Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da kai samame kan ƙungiyoyin masu aikata laifukan ta’addanci tare da roƙon al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.

By ukarofi