Yadda rikici ya kunno kai a APC ta Jigawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

A Jihar Jigawa, da ke arewa maso yammacin Nijeriya wani sabon rikici ya ɓarke a Jam’iyyar APC, mai mulkin jihar bayan da jam’iyyar ta sanar da dakatar da wani ɗan majalisar wakilai da wasu mutum shida bisa zarginsu da yi mata zagon ƙasa.

A cewar jam’iyyar, abubuwan da ake zargi sun haɗa da ayyukan da ka iya jawo wa mata zargi, da raunana ikon shugabanci tare da haifar da rarrabuwar kai a tsakanin ‘yan jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce dakatar da ɗan majalisar da ke wakiltar Hadejia da Auyo da Kafin Hausa, a majalisar wakilai ta tarayya, Usman Ibrahim Kamfani, bayan da wasu yan jam’iyyar a ƙaramar Hukumar Auyo suka shigar da ƙorafi a kan wasu maganganu da aka ce ya yi waɗanda suke zargin za su iya haifar da rikici a jam’iyyar.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar ta Jigawa, Bashir Kundu ya sheda wa BBC dalilin ɗaukar wannan mataki na dakatar da ɗan majalisar da wasu mutane shida:

”Ayarin wasu samari ne a karamar hukumar, Auyo suka yi taro inda suke cewa tun da nasu bai samu takara ba, ba a yi wa dansu adalci ba, wato dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Auyo da Kafin Hausa da kuma Haɗejia wato Kamfani Auyo, suka ce ba za su yi jam’iyyar ba kuma sai sun kai ta ƙasa.

”A kan haka aka kawo mana korafi, mu kuma muka ga ba za mu yarda da siyasar cin mutunci ba, ko ma waye idan ya taka mutum don yana da wani muƙami za mu ladabtar da shi.

”Saboda haka aka kawo mana korafi muka rubuta takarda nan take muka sanar da su mun dakatar da su har ma da shi dan majalisar mai ci, an dakatar da shi saboda shi ya kawo wannan fitina, da sauran mutum shida.,” inji Sakataren Bashir Kundun.

Sauran waɗanda aka dakatar sun haɗa da, Hajiya ‘Yargabi Babannan Auyo da Musa Idris Zabarau, da Ibrahim Ayama, da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Auyo da Saje Hadiyau da Sani Abdullahi Hadiyau, sai kuma Aisha Adamu Kande, wacce ke riƙe da muƙamin Mataimakiyar Shugabar Mata ta APC a jihar ta Jigawa.

Sai dai a martanin da ta mayar kan wannan dakatarwa da aka yi musu har ma da dan majalisar, Aisha Adamu Kanden ta musanta zargin da aka yi musu da cewa masu haɗa husuma ne kawai suka yi wannan kutungwila.

”Wallahi mu ba wani anti-party da muka yi saboda da Kamfani da danmodi tare muka gan su. ɗanmodi ubangidanmu a siyasa, Kamfani ubangidanmu ne a siyasa. Kuma mu dai a saninmu Kamfani Auyo ba ya wata jam’iyya face APC.”

”To daga baya sai aka kira mu aka ce mun je ana zagin gwamna muna gurin, muna farin ciki. Na ce wallahi ba gwamna ba, ko wanda bai kai gwamna ba in dai babba ne yana da shekaru, ba ta yadda zan ci mutuncinsa. Siyasa ce fa haduwar duniya rabuwar duniya. Amma duk wata magana da za a fada wallahi ba gaskiya ba ne,” in ji Kanden.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa matakin dakatarwar zai ci gaba da aiki har sai an kammala bincike inda za a fitar da mataki na gaba.

Duk wani ƙoƙari na tuntuɓar ɗan majalisar tarayyar da aka dakatar daga APCn, Usman Ibrahim Kamfani Auyo hakan ba ta cimma ruwa ba.

Shi dai Kamfani Auyo ya shafe shekara 12 yana wakiltar ƙananan hukumomin Auyo da Hadejia da Kafin Hausa a majalisar Wakilai ta Nijeriya, kuma rahotanni na cewa wannan taƙaddama ta samo asali ne, bayan da aka cimma masalahar sauya shi da wani wanda zai yi takarar majalisar a zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply