Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta kama mutane 225 bisa aikita laifuka daban daban da suka hada da fyaɗe da luwadi ,fashi da makami,dillancin ƙwayoyi da sauran su.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu a Katsina ya faɗi haka a lokacin da yake hira da manema labarai a madadin kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar Fage.
Ya ce a cinkin su mutane 36 ana zargin su da laifin aikita fyaɗe da luwadi da kuma mutane 21 da aka samu da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.
DSP Aliyu Sadiq ya bayana cewa yan sanda sun kama mutane 10 bisa zargin aikata fashi da makami sai mutane bakwai da suka ƙware wajen garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa.
Ya ce cikin waɗanda yan Sanda suka kama, sun saurari mutane 150 a cikin masu laifin,haka kuma sun gurfanar da mutane 109 a gaban kotu.
DSP Abubakar Sadiq ya sanar da cewa rundunar yan sanda a Katsina sun sami nasarar ceto mutane 17 daga hannu masu garkuwa da mutane da dabbobi guda 466 daga ɓarayin shanu.
Sun juma gano motoci da baburan hawa tare da miyagun ƙwayoyi kala kala harda tabar wiwi a cikin buhunna.
DSP Abubakar Sadiq ya jaddada ƙudirin kwamishinan yan sanda CP Ali Umar Fage na ganin ya magance aikata miyagun ayyuka a faɗin jihar.
Kwamishinan ya jinjinawa jami’an sa kan yadda suke nuna ƙwarewa da ƙwazo wajen tunkarar ɓata gari a jihar.
