Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Ayyuka, Sanata Injiniya David Umahi, ya bayyana cewa manyan ayyukan tituna guda huɗu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar a matsayin ayyukan gadonsa za su samar da wata babbar hanyar sufuri da za ta haɗa dukkan shiyyoyin Nijeriya guda shida, tare da bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa wadatar abinci da haɓaka haɗin kai tsakanin yankuna.
Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin tawagar Bankin Raya Zuba Jari da Ci Gaban Tattalin Arzikin Ƙasashen ECOWAS (EBID) ƙarƙashin jagorancin shugabar Sashen Ababen More Rayuwa na Asali a Ma’aikatar Kamfanonin Gwamnati ta bankin, Maimouna Sidibe.
Tawagar bankin na gudanar da bincike da tantancewa gabanin amincewa da ba da tallafin kuɗi ga Sashe na Farko na Babbar Hanyar Trans-Sahara, wadda ke cikin manyan ayyukan gadon Shugaba Tinubu.
Da yake maraba da tawagar, Ministan ya ce an tsara dukkan ayyukan titunan gadon shugaban ƙasar ne ta yadda za su kasance a matsayin wata babbar hanyar sufuri mai haɗa sassan ƙasar baki ɗaya.
“Dukkan ayyukan gadon Shugaban ƙasa guda huɗu suna haɗuwa ne a cikin wata madauwariyar hanyar sufuri,” inji Umahi.
Ya bayyana cewa Babbar Hanyar Gabar Tekun Lagos zuwa Calabar mai tsawon kilomita 750 tana haɗuwa da Babbar Hanyar Trans-Sahara ta hanyar yankin Ndibe Beach da ke Jihar Kuros Riba.
A cewarsa, Sashe na Farko na wannan hanya yana da tsawon kilomita 123.64 daga Ndibe Beach zuwa iyakar Jihar Benuwe, yayin da aka riga aka bayar da kwangilar wasu sassan da za su ratsa jihohin Benue, Kogi da Nasarawa.
Umahi ya ce wannan hanya ta daɗe tana wanzuwa tun zamanin mulkin mallaka, kuma tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kasuwanci da jigilar amfanin gona.
“Wannan hanya muhimmiyar hanyar samar da abinci ce ga ƙasa, kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wadatar abinci a Nijeriya,” inji shi.
Ministan ya ce aikin zai haɗa manyan yankunan noma na jihohin Ebonyi, Benuwe da Kuros Riba, tare da rage lokacin tafiya daga Kalaba zuwa Abuja zuwa kusan sa’o’i huɗu kacal.
“Wannan wata muhimmiyar hanyar tattalin arziki ce da za ta sauƙaƙa zirga-zirga da kasuwanci,” inji Umahi.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na da shirin amfani da madatsun ruwa da ke kan hanyar domin bunƙasa noman ban ruwa da samar da makamashi mai sabuntawa.
A cewarsa, hakan zai samar da sabbin masana’antu, jawo zuba jari da kuma samar da ayyukan yi masu yawa.
