Har yanzu Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Janar Rabe na hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majiyoyi sun bayyana cewa, har yanzu Hajiya Amina Abubakar, wato matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), tana hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

An yi awon-gaba da ita ne tare da marigayin mijin nata a lokacin da aka yi wa motarsu kwanton-ɓauna akan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafin-Soli da ke Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina a ranar 30 ga watan Mayu, 2026.

An ga Manjo Janar Rabe ne karo na ƙarshe a wani faifan bidiyo da ‘yan bindigar suka buƙaci a sako wasu abokan aikinsu da dabbobin da aka ƙwace a matsayin fansar mutanen biyu.

A faifan na tsawon minti huɗu ne aka ga tsohon sojan tare da Hajiya Amina suna bayanin buƙatar waɗanda suka sace su. A nan ta ce suna neman a sako Sani, Aminu da Nasiru da aka kama a Jiƙamshi da Kano.

Haka kuma, ta roƙi gwamnatin Jihar Katsina da jagororin ƙananan hukumomi biyar da su bayar da haɗin kai ga buƙatun domin su samu su shaƙi iskar ‘yanci.

Saidai, a wata sanarwa, Kwamishinan Tsaro da Lamuran Cikin Gida, Nasiru Mu’azu ya sanar da cewa Janar Rabe ya rasu ne sakamakon matsalolin cutar suga da hawan jini.

Kazalika, majiyoyin tsaro sun ce ana yunƙurin ceto hajiyar, amma ba su bayar da ƙarin bayani akan al’amarin ba.

By Babaji

Leave a Reply