Iyabo Obasanjo ta fice daga APC watanni biyu bayan rasa rikitin takarar gwamnan Ogun

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohuwar Sanata kuma mai neman takarar gwamnan Jihar Ogun, Farfesa Iyabo Obasanjo, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tana mai zargin shugabannin jam’iyyar a jihar da nuna mata rashin mutuntawa, wariya da kuma muzgunawa.

Iyabo Obasanjo, wadda ita ce babbar ‘yar tsohon Shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ta bayyana matakin nata ne a cikin wata wasiƙar murabus da ta aika wa Shugaban APC na Jihar Ogun, Cif Yemi Sanusi, mai ɗauke da kwanan watan 31 ga Mayu, 2026.

Tsohuwar ‘yar majalisar dattawan ta soki tsarin da ya bai wa Sanata Solomon Adeola, wanda aka fi sani da Yayi, tikitin takarar gwamna na jam’iyyar, tana mai cewa tsarin sasanci (consensus) da aka bi bai yi daidai da ƙa’idojin APC ba.

Ta ce duk da cewa ta amince za ta mara wa duk wanda ya fito ta hanyar sasanci baya, ba a tuntuɓe ta ko shigar da ita cikin shirin kafin a ayyana Adeola a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ba.

Iyabo ta kuma yi zargin cewa an hana wasu daga cikin magoya bayanta shiga wajen da aka bayyana ɗan takarar, tare da fuskantar barazana da tsangwama yayin gudanar da taron.

Duk da haka, ta bayyana cewa ta amince da sakamakon domin tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyar, inda ta gaggauta taya Adeola murna a daren da aka sanar da nasararsa.

A cewarta, daga baya Sanata Adeola ya nemi ganawa da magoya bayanta, inda suka gabatar masa da buƙatu uku. Sai dai ta ce duk da alƙawarin da ya yi na mayar da martani cikin mako guda, har bayan fiye da watanni biyu babu wata amsa da aka samu.

Ta bayyana cewa wannan lamari ya ƙara tabbatar mata da yadda ake ci gaba da nuna mata rashin kulawa da rashin yaba gudunmawar da ta bayar a jam’iyyar.

“Na amince da goyon bayan duk wanda ya samu tikiti ta hanyar sasanci, amma ba a tuntuɓe ni ba kafin a bayyana Sanata Adeola. An kuma hana wasu daga cikin magoya bayana shiga wurin taron tare da tsoratar da su. Duk da haka, na amince da sakamakon domin haɗin kan jam’iyya kuma na taya shi murna a daren da aka sanar da shi,” in ji ta.

Iyabo Obasanjo ta ce irin yadda aka yi watsi da ita bayan zaɓen fidda gwani ne ya sa ta yanke shawarar barin jam’iyyar.

Sai dai ta gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugabannin APC na Jihar Ogun da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar bisa goyon baya da karamcin da suka nuna mata a lokacin da take cikinta.

Iyabo ta koma siyasa a farkon shekarar nan bayan ta yi rajista a APC a Mazaba ta 11 da ke Ibogun, a ƙaramar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun. Ta taba zama Kwamishinar Lafiya ta jihar daga 2003 zuwa 2007, sannan ta wakilci Ogun Central a Majalisar Dattawa tsakanin 2007 da 2011.

Bayan ta gaza samun wa’adin mulki na biyu a 2011, ta koma Amurka inda ta rage shiga harkokin siyasa har zuwa ƙarshen shekarar 2025, lokacin da allunan yaƙin neman zaɓenta suka fara bayyana a sassan jihar Ogun, lamarin da ya nuna aniyarta ta komawa fafatawa a zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Daga bisani ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin APC, kafin daga bisani ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar.

By ukarofi