Daminar 2026: Jihohi 33 da Abuja na fuskantar barazanar ambaliya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da damina ke ƙara ƙarfi a sassa daban-daban na Nijeriya, fargaba na ƙaruwa kan yiwuwar ambaliyar ruwa, toshewar magudanan ruwa, raba jama’a da muhallansu da kuma ɓarkewar cututtuka a jihohi da dama. Duk da gargaɗin da hukumomi ke yi tun da wuri, masana na nuna damuwa kan ko ƙasar ta ɗauki matakan da suka dace domin kauce wa maimaita bala’o’in da aka sha fama da su a shekarun baya.

A farkon wannan shekara, Gwamnatin Tarayya ta fitar da Rahoton Hasashen Ambaliyar Ruwa na Shekarar 2026, wanda Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta ƙasa (NiHSA) ta gabatar a Abuja. Rahoton ya yi hasashen cewa jihohi 33 da Babban Birnin Tarayya Abuja za su iya fuskantar barazanar ambaliya a matakai daban-daban.

Rahoton ya bayyana cewa al’ummomi 14,118 da ke cikin ƙananan hukumomi 266 na cikin yankunan da ke cikin babban haɗari, yayin da wasu al’ummomi 15,597 a ƙananan hukumomi 405 ke cikin matsakaicin haɗari. Haka kuma, al’ummomi 923 da ke ƙananan hukumomi 77 na fuskantar ƙananan barazanar ambaliya.

Yayin da yake gabatar da rahoton, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli, Injiniya Joseph Utseɓ, ya jaddada muhimmancin tsarin gargaɗin gaggawa wajen rage asarar rayuka da dukiyoyi. 

Ya ce, samun bayanai cikin lokaci na iya taimakawa wajen kare rayuka, hanyoyin samun abinci da kuma muhimman kayayyakin more rayuwa.

Rahoton ya kuma yi hasashen yiwuwar ambaliyar gaggawa a manyan birane irin su Abuja, Legas, Ibadan, Kano da Fatakwal, sakamakon mamakon ruwan sama, rashin ingantattun magudanan ruwa da kuma gazawar tsarin tsara birane.

A yankunan bakin teku da koguna kuwa, jihohin Bayelsa, Delta, Legas, Ribas da Ogun na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa sakamakon tashin matakin teku da karuwar igiyoyin ruwa.

Ministan ya bayyana cewa rahoton ba wai takarda ce ta kimiyya kawai ba, illa wata kira ce ga gwamnatoci da al’umma da su ɗauki matakan kariya. Ya buƙaci gwamnatocin jihohi su haɗa batun kariyar ambaliya cikin shirye-shiryen amfani da ƙasa, su inganta magudanan ruwa tare da shirya al’ummomin da ke cikin haɗari.

Ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatarsa na aiki tare da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) domin inganta daidaiton hasashen yanayi ga manoma, masu tsara birane da masu kula da harkokin bala’o’i.

Bayan fitar da rahoton, gwamnatocin jihohi da dama sun fara aiwatar da matakan kariya.

A jihar Sakkwato, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) ta fara kai ziyara zuwa al’ummomi, tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma tantance yankunan da ke cikin haɗari. Daraktan Agaji da Gyaran Rayuwa na hukumar, Alhaji Mustapha Umar, ya ce ana shirya wuraren kwashe jama’a da matsugunan wucin-gadi tare da wayar da kai ga al’umma.

A Benue, gwamnati ta fara yaɗa saƙonnin faɗakarwa ta gidajen rediyo da kuma samar da lambobin gaggawa kyauta domin ƙara shirin ko-ta-kwana.

Jihar Kano kuma ta fara aiwatar da babban tsarin magudanan ruwa na birane tare da ci gaba da aikin share magudanan ruwa domin cire abubuwan da ke toshe hanyoyin ruwa.

A Kebbi, an sake farfaɗo da ƙungiyoyin ba da agajin gaggawa, an ƙara wayar da kan jama’a tare da tara kayan agaji domin tunkarar duk wani yanayi na gaggawa.

Jihar Kogi ta fara kafa cibiyoyin gudanar da ayyukan gaggawa, yayin da Adamawa ke ci gaba da wayar da kai musamman a yankunan da ke kusa da koguna, tare da shawartar jama’a su kauce wa zama a filayen da ruwa kan mamaye.

A Kwara, an fara shirye-shiryen kai ziyara ga yankunan da ke cikin haɗari, yayin da Edo ke haɗa aikin share magudanan ruwa da gyaran sansanonin ’yan gudun hijira da kuma tanadin wuraren matsuguni.

Jihar Neja kuwa na mayar da hankali kan ambaliyar gaggawa a Minna, Bida, Mokwa da Suleja, inda ake amfani da sarakunan gargajiya da masu aikin sa-kai wajen wayar da kan jama’a.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Ministan Muhalli Balarabe Lawal ya wakilta, ya yi kira ga dukkan matakan gwamnati da su haɗa kai wajen tunkarar barazanar ambaliya.

A nata ɓangaren, Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta ƙasa (NiHSA) ta inganta tsarin sa ido kan ambaliya zuwa tsarin bayar da bayanai kai tsaye, yayin da NiMet ta ƙara inganta hasashen yanayi ta hanyar amfani da fasahohin zamani.

An kuma ƙaddamar da wata manhajar wayar hannu domin isar da saƙonnin gargaɗi ga jama’a cikin lokaci.

Babbar Daraktar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, ta bukaci gwamnoni musamman na yankin Kudu maso Kudu da su ɗauki matakan kariya tun kafin ambaliya ta afku.

Ta bayyana cewa hukumar ta samar da Tsarin Gudanar da Haɗurran da Sauyin Yanayi ke Haifarwa na 2026, wanda ya haɗa da shirye-shiryen kwashe jama’a, atisayen gwaji, share magudanan ruwa da kuma tsarin kariya a matakin al’umma.

Duk da waɗannan matakai, masana na ganin har yanzu akwai babban giɓi tsakanin hasashen da ake yi da kuma aiwatar da matakan kariya.

Wani ƙwararren masanin harkokin ruwa, Dakta Peter Onouha, ya ce Nijeriya na ci gaba da maimaita tsohon kuskure na yin gargaɗi ba tare da ɗaukar matakan kariya ba.

A cewarsa, hukumomi irin su NiMet da NiHSA na fitar da sahihan gargaɗi a kai a kai, amma galibin gwamnatocin jihohi ba sa juya waɗannan bayanai zuwa matakan kariya a ƙasa.

Ya bayyana cewa sakamakon hakan shi ne yawan rasa gidaje, lalacewar dukiyoyi da mutuwar jama’a da za a iya kauce wa.

Dakta Onouha ya ce wayar da kai bai kamata ta zama ta lokacin damina kawai ba, ya kamata ta kasance aiki mai dorewa. Ya kuma yi kira da a ƙarfafa isar da saƙonni cikin harsunan gida domin al’ummomin karkara su fahimci haɗarin da ke gabansu.

Masana harkokin lafiya sun yi gargaɗin cewa ambaliya ba ruwa kaɗai ba ce, domin tana ɗauke da ƙazanta, sinadarai masu guba da ƙwayoyin cututtuka.

A cewarsu, bayan kowace ambaliya ana fuskantar ɓarkewar cututtuka irin su kwalara, zazzaɓin taifod, cutar hanta nau’in A da E, zazzaɓin cizon sauro da wasu cututtukan da ke yaɗuwa ta ruwa.

A shekarar 2024 kaɗai, Nijeriya ta samu sama da mutum 11,000 da suka kamu da kwalara, yayin da daruruwan mutane suka mutu sakamakon cutar.

Masana sun shawarci jama’a da su tsaftace ruwan sha, su guji hulɗa kai tsaye da ruwan ambaliya, su rufe raunuka, su kawar da ruwan da ke taruwa kusa da gidaje tare da amfani da gidan sauro.

Masana sun ce tushen matsalar ya ta’allaka ne ga rashin ingantattun magudanan ruwa, gazawar tsara birane yadda ya kamata, gina gine-gine a wuraren da bai kamata ba da kuma tasirin sauyin yanayi.

A birane irin su Abuja, Legas, Kano, Fatakwal da Kaduna, yawaitar gine-gine ba tare da bin ƙa’ida ba da kuma lalacewar wuraren shan ruwa na ƙara haddasa matsalar ambaliya.

Masana harkokin ruwa sun bayyana cewa ambaliya ba hatsari ba ne da ke faruwa kwatsam, illa sakamakon gazawar tsare-tsare da rashin kula da muhalli.

Yayin da Nijeriya ke shiga tsakiyar daminar 2026, abin da ya fi bayyana shi ne cewa matsalar ba ta hasashen ambaliya ba ce, domin ana samun bayanai tun da wuri. Babban ƙalubalen shi ne yadda za a mayar da waɗannan gargaɗi zuwa aiki domin ceton rayuka da dukiyoyi.

By ukarofi

Leave a Reply