Yadda marubuta ke ba da gudunmawa ga zaman lafiya

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

A ƙarshen watan da ya gabata, haɗakar ƙungiyoyin marubutan adabi na Jihar Filato da ake yi musu laƙabi da COPLIS, ƙarƙashin ƙungiyar Marubutan Nijeriya ta ANA Plateau, suka gudanar da babban taron shekara-shekara da suka saba yi, domin tattauna gudunmawar marubuta da ƙalubalensu, rubutattun waƙoƙi, raye-raye da bajekolin kasuwar littattafai.

Baƙi daga ciki da wajen Jihar Filato har ma da ƙetaren Nijeriya sun samu halartar taron, wanda aka yi wa taken, “Yadda rubutun adabi zai inganta zaman lafiya a Filato da wajenta.” Taron, wanda shi ne irinsa na uku da aka shirya da nufin haɗa kan marubuta na da da na yanzu, domin yin aiki tare yadda sunan Jihar Filato, al’adun al’ummarta, da fasahohinsu za su yaɗu a duniya.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Babban Sakataren ƙungiyar Marubuta ta Pan Afirca, Dakta Wale Okediran, da Dakta Carmen McCain wata malamar jami’a mai nazari kan rubuce-rubucen adabi na ’yan Afirka, musamman a ɓangaren adabin Hausa da finafinai, wacce ta zo daga birnin Landan, da kuma ƙwararriyar malamar adabi daga Jami’ar Abuja mai koyar da adabin Turanci da nazari kan rubuce-rubucen adabi a Afirka, Dakta Zaynab Ango, sai fitaccen marubuci kuma malamin jami’a, Farfesa Dhul Johnson, da Farfesa Kaze Afan na Jami’ar Jos, da Dakta Sunusi Shehu ƙwararren masanin adabi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi. 

Taron ya kuma gayyato marubuta littattafan adabi da ƙungiyoyin marubuta da suke ba da gudummawa a harkar rubuce-rubuce, kamar irin su ƙungiyar shirya bajekolin littattafai ta Jos Book Fair, ƙungiyar Jos Writers Club, da ƙungiyar Plateau Writers Society da sauransu.

Yayin taron an tattauna game da gudunmawar da marubuta ke bayarwa ga cigaban zaman lafiya, duba da irin yanayin da Jihar Filato ke ciki tsawon lokaci, game da rikice-rikicen ƙabilanci da na addini, zuwa ta’addancin ’yan bindiga masu kai hare-hare a ƙauyuka da gonaki. Harwayau, an duba batun yadda marubuta za su iya magance matsalar nuna wariya a siyasa ta yadda kowanne ɓangare na al’umma zai samu damar ba da gudummawa. Akwai kuma gasar rubutun ƙagaggun labarai da aka shiryawa ’yan makarantun sakandire, wanda fitaccen marubucin nan kuma ɗan siyasa, Dr. Chris Kwaja yake ɗaukar nauyin shiryawa duk shekara. 

Sannan kuma Dr. Carmen McCain ta gabatar da lacca game da ƙalubalen fassara da muhimmancin ta wajen yaɗa rubuce-rubuce da aka yi cikin harsunan gida na Afirka zuwa Turanci da kuma mayar da na Turanci zuwa ga harsunan gida don sauƙaƙawa masu karatu fahimtar saƙon da marubucin ke son isarwa ga jama’a. Wanda ya ƙayatar sosai, domin a wajen an samu waɗanda suka yi ƙoƙarin fassara wani sashi na littafin Umar Turaki na Turanci, ‘Eɓery Drop of Blood is Red’, da kuma littafin Hausa na Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, ‘Wa Zai Auri Jahila?’ Zuwa harsunan su na gado, kasancewar Jihar Filato jiha ce mai ƙabilu da yawa. Har ma an samu masu fassara daga Hausa zuwa Larabci da Faransanci.

Lacca ta musamman da ta fi ɗaukar hankali a taron ita ce wacce ta duba taken taron, wanda kuma Dr Zaynab Ango daga Jami’ar Abuja ta gabatar. A cikin laccar an tattauna muhimmancin girmama al’adu da addinan juna, da bai wa kowa damar bayyana fahimtarsa da gudummawarsa. Ta bayar da misalai na yadda marubuta a Afirka ke ƙoƙarin gabatar da koke-koken al’ummarsu da ‘yancinsu, da yadda suke ƙoƙarin sauya tunani da zamantakewar al’ummarsu.

Farfesa Dhul Johnson, jagoran marubuta a Jihar Filato ya yi tsokaci kan muhimmancin marubuta a cikin al’umma, inda ya ce marubuta kamar kadara suke a cikin al’umma. Ya ƙara da cewa, gudunmawar marubuta ce ta taimaka wajen ƙato ýancin wasu ƙasashen Afirka a lokacin mulkin mallaka. Ba don su ba, a cewarsa da Afirka ta daɗe a cikin duhu da ƙangin bauta.

Babu shakka taron ya ƙayatar sosai, ya zarta na shekarun baya wajen cika da halartar manyan baƙi da suka samu halarta daga kusa da nesa. Manyan malaman jami’a maza da mata sun samu bayar da gudummawa. Marubuta da masu shirya finafinai da nishaɗantarwa irin su Danja Abdullahi, Nathan Biɓan, da Hussaini Zaguru, da Kenneth Gyang sun ƙara wa taron armashi sosai.

Kodayake taron ya zo daidai lokacin da ake gudanar da zaɓen fitar da ’yan takara na jam’iyyar APC, wanda hakan ya hana wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Jihar Filato samun damar halarta, amma gudunmawar da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Caleb Manasseh Mutfwang, ta taimaka sosai wajen samun nasarar taron. 

Sannan shugaban ƙungiyar haɗakar ƙungiyoyin marubutan da suka shirya bikin, ɓictor Meshak Jatau ya bayyana cewa, gwamnatin ta ware kuɗi don sayen filin da za a gina lambun karatu na gwamnati, kamar yadda Gwamnan ya yi alƙawari, sai dai rashin samun zarafin Gwamnan ya hana a ƙaddamar da aikin ginin kamar yadda aka tsara cikin tsare-tsaren abubuwan da za a gabatar na wannan shekarar. 

Muna fata bikin bajekolin fasahohin marubuta na shekara mai zuwa zai ƙara inganta da kuma jawo hankalin marubuta daga sassan duniya daban-daban.

By ukarofi