Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa ya ɗauki sababbin matakai domin inganta tsaro da magance matsalar ‘yan bindiga masu sace jama’a, lamarin ya biyo bayan matakan da hukumomi suka ce za su ɗauka bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar (Mai ritaya) a hannun masu garkuwa da mutane.
Daga cikin matakan tsaro da gwamnati ta ɗauka akwai hana sana’ar POS da cajin waya a wasu ƙananan hukumomin jihar da rashin tsaro ya yi ƙamari.
Gwamnatin jihar ta ce ta fitar da wannan haramci da nufin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar, musamman a yaƙin da ake yi da ɓarayin daji masu garkuwa da mutane.
Gwamnan ya sanar da matakan ne bayan wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar tare da hukumomin tsaro, shugabannin gargajiya, da muhimman masu ruwa da tsaki.
Mai magana da yawun gwamna Dikko Raɗɗa, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne bayyana matakan da aka ɗauka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Gwamnatin Katsina ta sanar da cewa ta haramta sayarwa, saye, safara da ajiyar man fetur a cikin jarkoki a duk faɗin jihar nan take. Ta ce:
“An ɗauki wannan matakin ne domin hana karkatar da man fetur zuwa hannun masu aikata laifuffuka da ke ta’addanci a yankunan karkara.”
Gwamnan ya kuma amince da rufe kasuwancin POS da wuraren cajin wayoyin hannu a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa nan take.
Gwamnatin Katsina ta kafa hujja da cewa
“Binciken tsaro ya nuna cewa ana amfani da waɗannan wurare ta hanyar da ke taimaka wa ƙungiyoyin masu laifi wajen gudanar da ayyukansu.”
Bugu da ƙari, an haramta amfani da babura a dukkan ƙananan hukumomin Matazu da Musawa
“An sanya wannan takunkumin ne domin katse zirga-zirga da ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane waɗanda galibi ke dogaro da babura wajen sufuri.” In ji sanarwar
Daga ƙarshe gwamna raɗɗa ya yi kira ga al’umma da su mara wa hukumomi baya ta hanyar bin umarnin tare da bayar da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro duk lokacin da hakan ya taso.
