Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kai ziyarar bazata a garin Matazu da sauran al’ummomin da ke kewaye da yankin ƙaramar hukumar Matazu, domin duba halin tsaro da kuma yadda ayyukan tsaro ke gudana.
Ziyarar ta zo ne bayan gabatar da rahoton tsaro da tattaunawa da kwamandan rundunar sojojin, Manjo Janar W. B. Idris, gami da aiwatar da umarnin shugaban ƙasa na ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ke fuskantar barazana a faɗin jihar Katsina.
A yayin rangadin, gwamnan ya fara ziyartar garin Matazu kafin ya wuce zuwa Sayaya, sannan ya ci gaba zuwa garuruwan Mazoji, Fafawa, Nasarawan Kalgo, da kuma Tashar Icce.
A waɗannan wurare, ya ga yadda mazauna yankin ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, wanda hakan ke nuni da ingantuwar tsaro a wuraren.
Ya Kuma zagaya sauran al’ummomin da ke makwabtaka da ita, inda ya lura da yadda aka tura jami’an tsaro da sojoji masu yawa, waɗanda aka ajiye su bisa dabarun tsaro a muhimman hanyoyi da kuma mazaunai.
Haka zalika, Gwamnan ya bi ta hanyar Mazoji zuwa Dutsinma kafin ya koma Katsina, inda ya ga yadda jami’an tsaro ke ci gaba da sintiri tare da haɗin gwiwa a kan hanyar.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana gamsuwarsa da yadda jami’an tsaro suke gudanar da aiki tare da bayyana kansu a fili yayin rangadin, inda ya lura cewa al’umma na ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba.
Ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro bisa sintirin da suke yi da kuma dabarun tura jami’ai a inda ya kamata, inda ya bayyana hakan a matsayin wani babban mataki na tabbatar da dauwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar Katsina.
Garin Matazu ya zama wani mararrabar yan bindiga ƙarƙashin jagorancin Muhammadu kachalla inda aka kashe Manjo Janaral Rabe Abubakar mai ritaya
