Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi ta samu nasara wurin yaƙi da ta’addanci da garkuwa da jama’a da mallakan makamai ba’a kan ƙa’ida ba.Da yake ma manema labarai bayani a hedkwatar rundunar dake Birnin Kebbi ranar Laraba, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Umar Hadejia, ya fayyace cewar ‘yan ta’addan Lakurawa da Mamudawa da Boko Haram 12, da kuma wanda aka kama da laifin fyaɗe suna nan kulle wurin ‘yan sanda, ana share fagen gurfanar dasu gaban kotu.
“A ranar 5 ga Yuni 2026, ‘yan sandan mobile da ke ofishin ‘yan sanda na Illo, a ƙaramar hukumar Bagudo, sun kama ‘yan kungiyar Mamudawa/Boko Haram guda uku, Muhammadu Bandi, Aliyu Abubakar da Muhammadu Abubakar”,
“An cafke su ne suna kan babur zuwa garin Lolo, ana zarginsu da zuwa sawo ma ‘yan’uwansu ‘yan ta’adda kayan abinci”,
“Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewar waɗanda ake tuhumar, suna da masaniya a kai-komon da aka yi da ya yi sanadiyyar kisan gilla da aka yi ma jami’an hukumar kare haɗura ta ƙasa guda uku a Illo, a ranar 4 ga watan Yuni”,
“Haka kuma, a ranar 7 ga Yuni, ‘yan sandan mobile da ke sintiri na musamman akan hanyar Ka’oje zuwa Bakin Ruwa dake ƙaramar hukumar Bagudo, sun cafke wasu da ake tuhuma mutum huɗu, Haruna Abubakar, Abubakar Lawali, Anme Shehu da Yahaya Shehu”,
“Ana gudanar da bincike akansu dangane da tuhuma mai ƙarfi dangane da hannu a harkokin ta’addaci da akeyi a cikin gandun-daji na SODA”, cewar Kwamishinan.
Hadejia ya kuma sanar da kama wani mai suna Murtala Sani na ƙauyen Zazzagawa bisa tuhumar da ake mashi cewar shine hadimin ‘yan ta’adda wanda suke aikawa yana sawo masu kayan abinci da abin-sha.
Shugaban ‘yan sandan ya yi bayanin cewar bincike da aka fara gudanarwa, an lura cewar sau-da-yawa yakan ɗauki wani ɗan-ta’addan Lakurawa, Amadu Umar, daga ƙauyen Zazzagawa zuwa maɓoyarsa.
“A wani ɓangaren kuma, a ranar 10 ga Yuni, wasu gungun mutane ɗauke da makamai sun kai farmaki a yankin bayan Forestry, dake Birnin Kebbi, suka kutsa kai gidan Mustafa Musa”,
“Gungun mutanen na ɗauke da bindigogi da adduna da kuma sanduna, suka karya ƙofar gidan, suka shiga cikinsa suka sace kudi N220,000, da wayoyin hannu, sannan kuma, suka ɗauki matarsa, Asmau Isah, suka wuce da ita”,
“Nan take jami’an ‘yan sanda tare da haɗin-gwiwan zaratan Civilian JTF da Vigilante, sun yi nasarar ceto wannan matar aure, sannan kuma aka kama wani mai suna Abubakar Siddi”,
“A ranar 11 ga Yuni, ‘yan sanda da ke aikin sintiri na musamman a Bakin Ruwa, ƙaramar hukumar Bagudo, sun kama wani mai suna Ayuba Ibrahim, wanda ake tuhumar yana taimaka ma ɓatagari”,
” ‘Yan sanda sun kama shi da bindiga pump-action da albarusai guda uku masu-rai, da kuma wata jakka mai ɗauke da kayayyakin ayyukan ɓatagari”,
“Haka kuma, ‘yan sanda dake ofishin yanki na Makera, sun kama wani mai suna Aliyu Jibrin ɗan shekara 42, dan asalin ƙauyen Kwakware dake ƙaramar hukumar Arewa, kuma aka sameshi da bindigar hannu ƙirar gida (adaka)”,
“Sannan kuma, aikin haɗin kai tsakanin rundunar ‘yan sanda ta Kebbi da takwararta ta Sokoto sun gano wata motar da aka sace ƙirar marsandi C200, a Bayan-Kara da ke Birnin Kebbi, kuma aka kama wani mai suna Ahmed Sa’adu da ake ma laƙabin Baga, sannan kuma an sanya himma wurin kama abokin aikata laifinshi, Kasimu Bunza da sauran gungun mutanensu”,
“An miƙawa rundunar Sokoto motar da aka gano, wadda aka sace daga wani mazaunin Sokoto”,
“A wani labarin na dabam, ‘yan sanda sun kama wani mai suna Faruku Muhammed mai shekara 36 dake Tungar Zabarmawa, ƙaramar hukumar Jega, da laifin yaudarar wata ƙaramar yarinya mai shekara 10, zuwa ɗakinsa da ke cikin Makarantar Islamiyya a inda yake gadi yayi lalata da ita ta hanyar sanya yatsunsa a cikin farjinta”.
“Rundunar na ci gaba da ƙara ƙaimi wurin sintiri da kuma tura jami’an ‘yan sanda zuwa duk inda ɓatagari ke gudanar da munanan ayyukansu”, Kwamishinan yace.
