Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu (COOU) da ke Igbariam a jihar Anambra ta kori ma’aikata biyar bisa zargin aikata laifuka da suka haɗa da cin zarafin mata, tursasawa, barazana, karɓar kuɗi ta hanyar danniya da kuma rashin ɗa’a.
Daga cikin waɗanda aka kora akwai tsohon shugaban Sashen Shari’a, Farfesa C.C. Nwabachili, da Farfesa Chike Osegbue na Sashen Kimiyyar Siyasa.
Sauran waɗanda hukuncin ya shafa sun haɗa da ma’aikata daga Sashen Microbiology da kuma wata babbar jami’a mai mukamin Principal Assistant Registrar.
Jami’ar ta bayyana cewa an yanke hukuncin ne bayan nazari da amincewar kwamitin gudanarwa, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da ladabi, gaskiya da ɗaukar alhakin ayyuka a makarantar.
Haka kuma, jami’ar ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya aikata abin da zai ɓata mata suna zai fuskanci hukunci mai tsauri.
