
Farashin ɗanyen mai ya ragu ƙasa da Dala 75 a ranar Alhamis, karo na farko tun watan Maris, 2026, wato mafi ƙanƙantarsa tun lokacin da aka fara yaƙin Iran, bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Amurka da Iran ta ƙara hasashen samun wadataccen mai a kasuwannin duniya.
Farashin man Brent ya sauka da dala 1.59, wato kashi 2%, zuwa dala 77.96 kan kowace ganga, yayin da man West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya ragu da dala 1.83, wato kashi 2.38%, zuwa dala 74.96 kan kowace ganga.
Faduwar farashin ya biyo bayan yarjejeniyar mai matakai 14 da Amurka da Iran suka cimma, wadda ta tsawaita tsagaita bude wutar na tsawon kwanaki 60 domin ci gaba da tattaunawa tare da bude mashigin ruway Hormuz, wanda hanya ce mai muhimmanci wajen jigilar mai da iskar gas a duniya.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen dawo da fitar da man Iran zuwa kasuwannin duniya a hankali. Masana harkar makamashi sun ce ‘yan kasuwa sun fara lissafa yiwuwar dawowar man Iran cikin sauri.
Yarjejeniyar ta tanadi cewa zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz za ta koma cikakkiyar hanya cikin kwanaki 30, duk da cewa wasu manyan batutuwa kamar shirin nukiliyar Iran har yanzu ba a warware su ba.
Masana sun bayyana cewa farashin mai na iya ci gaba da raguwa, amma ba za a ga babban faduwa cikin gaggawa ba, saboda ƙasashe na sake cike ajiyar mai kuma bukatar makamashi a duniya tana nan daram.
Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta yi gargadin cewa dole ne tattaunawar ta yi nasara cikin kwanaki 60, bayan da ta taba cewa rufe mashigin ruwan Hormuz na dogon lokaci na iya jefa tattalin arzikin duniya cikin matsala.
Har ila yau, hasashen cewa Babban Bankin Amurka zai iya ƙara kudin ruwa a wannan shekara domin rage hauhawar farashi shi ma na iya rage bukatar mai ta hanyar takaita bunƙasar tattalin arziki.
