Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla manyan kwamandojin soja shida da ke bakin aiki tare da wani Manjo Janar mai ritaya guda ɗaya ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ’yan ta’adda da ’yan bindiga a Nijeriya tun daga farkon shekarar 2026, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a kan taɓarɓarewar matsalar tsaro a sassan ƙasar.
Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da kashe-kashe, sace-sacen mutane da hare-hare kan al’umma, makarantu da cibiyoyin tsaro a wasu yankuna na Nijeriya.
Duk da cewa fararen hula ne wannan matsala ta fi shafa, jami’an tsaro da kwamandojin soja da ke jagorantar ayyukan yaƙi da ta’addanci ma sun kasance cikin waɗanda hare-haren suka fi shafa.
Sabon lamarin ya shafi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda rahotanni suka ce ya rasu ne bayan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Jihar Katsina.
Kwamandojin Soja Shida Da Aka Kashe A 2026:
1. Laftanar Kanal O.C. Okolo
An kashe shi a ranar 16 ga Fabrairu, 2026 lokacin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari ƙauyen Mandaragirau da ke ƙaramar Hukumar Biu a Jihar Borno. Daga bisani an yi masa jana’iza a garinsu na Obinofia Ndiuno da ke ƙaramar Hukumar Ezeagu a Jihar Enugu a watan Afrilu.
2. Manjo U.I. Mairiga
Kwamandan sansanin soji na Mayenti a Jihar Borno ne. Ya rasu a ranar 1 ga Maris, 2026 bayan harin da mayaƙan da ke ɗauke da makamai suka kai masa.
3. Laftanar Kanal S.I. Iliyasu
An kashe shi a ranar 6 ga Maris, 2026 lokacin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari wani bataliyar soji a yankin Konduga na Jihar Borno.
4. Laftanar Kanal Umar Farouƙ
Ya rasa ransa a ranar 9 ga Maris, 2026 yayin wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai wani sansanin soja a Jihar Borno.
5. Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah
Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan ƙungiyar Daular Musulunci ta Yammacin Afirka (ISWAP) sun kashe shi a ranar 9 ga Afrilu, 2026.
6. Kanal I.A. Mohammed
Shine Kwamandan Bataliya ta 242 ta Rundunar Sojin Nijeriya da ke Monguno a Jihar Borno. Ya mutu ne yayin da yake bakin aiki a ranar 13 ga Afrilu, 2026.
Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya ya mutu a hannun ’yan bindiga:
Mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya ta ƙara jawo fushin jama’a kan halin rashin tsaron da ƙasar ke ciki. Duk da cewa ya yi ritaya daga aikin soja, rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne bayan ya shafe lokaci a hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Katsina.
An yi garkuwa da shi tare da matarsa a ranar 30 ga Mayu a hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke ƙaramar Hukumar Matazu.
Kafin sanar da rasuwarsa, an ga shi tare da matarsa a cikin wani bidiyo inda masu garkuwar suka bayyana wasu buƙatu.
A cikin bidiyon mai tsawon mintuna huɗu da daƙiƙa biyu da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ma’auratan sun bayyana cewa masu garkuwar sun buƙaci a saki wasu daga cikin mutanensu uku masu suna Sani, Aminu da Nasiru.
Matar marigayin ta ce biyu daga cikin mutanen an kama su ne a Jikamshi, yayin da aka kama na ukun a Kano.
Ta kuma roƙi Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi biyar da abin ya shafa da su taimaka wajen ganin an ceto su.
A wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu, ya fitar, ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana mutuwar marigayin a matsayin babban abin takaici.
Ya ce marigayin jami’in soja ne mai daraja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare Nijeriya da al’ummarta.
“Abin takaici ne ƙwarai cewa mutum da ya yi wa ƙasarsa hidima da mutunci, ya yi aiki har ya kai manyan mukamai a rundunar soji, sannan ya gamu da irin wannan mummunan ƙarshe a hannun masu aikata laifi,” inji Obi.
Ya ƙara da cewa mutuwar tasa wata babbar masifa ce ga ƙasa kuma shaida ce ta yadda matsalar tsaro ta yi ƙamari.
Shi ma tsohon Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), Sam Amadi, ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnati ta kasa ceto marigayin da matarsa.
A nasa bangaren, Shugaban Jam’iyyar ADC na ƙasa, Sanata Daɓid Mark, ya ce ’yan Nijeriya sun zama cikin haɗari a ƙasarsu sakamakon ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ba za ta miƙa wuya ga buƙatun ’yan ta’adda ba.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya ce duk da irin ta’asar da masu garkuwa da mutane suka aikata, gwamnati ba za ta saki mutanen da hukumomin tsaro ke tsare da su ba.
Ya kuma yi gargaɗi ga ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci ƙarfin ikon gwamnatin Nijeriya.
“’Yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci su miƙa wuya yanzu ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Nijeriya. Wannan damar ba za ta kasance a buɗe har abada ba, kuma ba za a nuna jinƙai ga masu zubar da jinin ’yan Nijeriya ba,” inji shugaban ƙasar.
