Likitoci sun gano katako a cikin kan wani mutum bayan shekaru biyu

Spread the love

Likitoci a ƙasar Rasha sun yi mamakin gano wani katako mai tsawon inci biyar a cikin kan wani mutum, shekaru biyu bayan ya samu hatsari yayin da yake aikin sare itatuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, katakon ya shiga ne ta kusa da idon mutumin bayan wani ɓangare na itace ya karye ya buge shi. Duk da raunin da ya samu a lokacin, bai fahimci cewa, wani ɓangaren katako ya maƙale a cikin kansa ba.

Bayan shekaru biyu, mutumin ya fara fama da matsanancin ciwon kai da kumburi, lamarin da ya sa ya garzaya asibiti. Bayan an yi masa gwaje-gwaje da hoton binciken likitoci suka gano katakon da ya maƙale a cikin kansa tun daga shekarar 2024.

An yi masa tiyata cikin nasara, inda aka cire katakon, kuma likitoci sun bayyana cewa, abin mamaki ne yadda ya rayu tsawon wannan lokaci ba tare da ya fuskanci matsaloli masu tsanani ba.

Lamarin ya jawo hankalin jama’a da dama, inda masana lafiya suka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ba kasafai ake gani ba a fannin likitanci.

By ukarofi

Leave a Reply