Daga MOHAMMED BALA GARBA
A ranar Laraba, 6 ga watan Yunin shekarar 2018, tsohon shugaban ƙasar Nijeriya marigayi Muhammadu Buhari ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni (June 12) a matsayin sabuwar ‘Ranar Dimokuradiyya’ a Nijeriya, maimakon 29 ga Mayu (29 May). Inda kuma ya ba wa M.K.O Abiola lambar yabo ta GCFR bayan mutuwarsa. Shin wacce rana ce June 12? Kuma me ya faru a cikinta?
June 12 rana ce ta tarihi, wacce ba za a taɓa mantawa da ita ba a Nijeriya. A ranar ne ɗan takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) wato Mashood Abiola ya fafata da ɗan takarar jam’iyyar National Republican Convention (NRC) Alhaji Bashir Tofa a babban zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 1993. Mataimakin Abiola shi ne Baba Gana Kingibe daga jihar Borno, yayin da Sylvester Ugoh daga jihar Imo ya yi wa Alhaji Bashir Tofa mataimaki.
Duk da cewa masu sharhi na ganin zaɓen June 12 shi ne zaɓe mafi inganci a tarihin zaɓukan Nijeriya, amma gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin (ƙarƙashin Gwamnatin Ibrahim Badamasi Babangida) ta soke zaɓen bisa zargin maguɗi; wanda hakan ya haifar da gangarumar zanga-zangar da ta tilastawa Babagidan sauƙa daga kan karagar mulki a ranar 26 ga August. Bayan ya sauƙa, aka kafa gwamnatin riƙon kwarya, ƙarƙashin jagorancin Cif Earnest Shonekan, wanda daga baya Janar Sani Abacha ya hamɓarar da shi a wani juyin mulki da ake kira da ‘juyin mulkin falo’ a ranar 17 ga watan November.
Dukkan alamu sun nuna jam’iyyar SDP ta su Abiola ita ce kan gaba wajen lashe zaɓen da aka soke, wanda wannan ya sa Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa a ranar 11 ga watan July ɗin 1994 a jihar Legas. Matakin da ya sa gwamnatin Abacha ta zarge shi da cin amanar ƙasa, tare da kama shi ta tsare a ranar 23 ga July. An tsare Abiola na tsawon shekaru huɗu a gidan yari, inda wasu rahotanni suka nuna ban da Alƙur’ani da Littafi Mai Tsarki (Bibble) Abiola ba shi da wata hanyar samun bayanai.
An zargi mutane bakwai da taka muhimmiyar rawa wajen soke wannan zaɓen na June 12. Waɗannan mutane su ne:
1- Ibrahim Badamasi Babangida:- shugaban mulkin soja wanda ya soke zaɓen da a kayi ittifakin shi ne zaɓe mafi tsafta a tarihin ƙasar.
2- Sani Abacha:- yana cikin mambobin kwamitin mulkin soja (AFRC) da suka soke zaɓen. An yi ikirarin cewa ya taka muhimmiyar rawar gani wurin soke zaɓen tare da rufe wanda ake ganin shi ya lashe zaben a kurkuku.
3- Arthur Nzeribe:- tsohon Sanatan da ya ba da babbar gudunmawa wurin soke zaɓen. Shi da Abimbola Davies suka kafa ‘Association for Better Nigeria’ ABN da ta nemi kotu ta dakatar da zaɓen wanda hakan ya bawa gwamnati damar soke zaɓen gabaɗaya.
4- Uche Chukwumerije:- yana cikin na hannun daman Abacha da suka riƙa goyon bayan kar a yi zaɓe a ƙasar.
5- Walter Ofonagoro:- shi ma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka riƙa adawa da masu gwagwarmayar June 12. Mutane suna yi masa laƙabi da kakakin gwamnatin Abacha saboda yadda yake kare ƙudirorin gwamnatin.
6- Lamidi Adedibu:- tsohon jigon siyasa a jihar Ibadan. Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi ƙaurin suna don adawa da gwagwarmayar June 12. Saboda ya daɗe yana amfana da gwamnatin soja kuma yana bawa gwamnati bayanai kan ayyukan ƙungiyar ‘National Democratic Coalition’ da ke gwagwarmayar June 12.
7- Abdulazzez Arisekola Alao:- duk ɗan kasuwa mazaunin Ibadan ba zai taɓa manta abin da ya faru da Abdulazzez a Jami’ar Ibadan ba a watan November 1998. Ya tafi jami’ar tare da tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalam Abubakar don hallartar bikin yayen ɗaliban jami’ar, amma ɗaliban jami’ar suka far masa suka ƙwace motocinsa suka ƙona su. Da kyar aka tseratar da shi a motar ‘yan sanda.
Darrusan da ke cikin ranar ‘June 12’
Darrusan da ke cikin abin da ya faru a ranar June 12 na shekarar 1993 su ne kamar haka:
1- Ikon jama’a – lokacin da ‘yan ƙasa suka haɗa kai, suna iya zaɓar wanda suke so ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba. Abiola ɗan Kudu ne, Musulmi, abokin takararsa Kingibe ɗan Arewa ne, Musulmi, amma Kiristocin Kudu da sauran su sun zaɓe su.
2- Hatsarin cin amanar al’umma – soke zaɓen da jama’a suka yi da gaskiya yana jefa ƙasa cikin ruɗani. Soke zaɓen June 12 ya koyar da mu cewa dimokuradiyya ba za ta yi tasiri ba idan masu mulki ba su girmama zaɓen jama’a ba.
3- Muhimmancin haƙuri da juriya – duk da an soke zaɓen, Nijeriya ta ci gaba da gwagwarmaya har ta dawo kan turbar dimokuradiyya a shekarar 1999. Yaki da zalunci yana buƙatar lokaci da sadaukarwa.
4- Dole a kare kuri’a – bayan 12 June, ‘yan Nijeriya sun ƙara kula da zaɓe. INEC, kotuna, da ƙungiyoyin farar hula sun fi ƙwazo wajen ganin an yi adalci.
5- Sadaukarwa – M.K.O Abiola ya rasa dukiyarsa, ‘yancinsa da kuma ransa, saboda ya tsaya kan gaskiya. Ya nuna cewa wani lokaci a ce “ku kama ni” don al’umma su samu ‘yanci.
A takaice, June 12 ranar tunawa da haɗin kan Nijeriya ce, da darajar kuri’ar talaka, da hatsarin mulkin kama-karya. Wannan shi ne (a taƙaice) abin da ya faru a ranar June 12 ɗin shekarar 1993 wanda gwamnatin Nijeriya ta mayar da ranar a matsayin ranar dimokuradiyya.
Mohammed Bala marubnuci ne a Maiduguri,
12 ga Yuni, 2026
