Hukumar SEC ta dakatar da shirin IPO na Matatar Ɗangote, ta gargaɗi ‘yan kasuwa

Spread the love

Hukumar Kula da Kasuwannin Hannayen Jari ta Ƙasa SEC, ta bayar da umarnin dakatar da duk wani tallace-tallace ko kamfen da ke da alaƙa da sayar da hannayen jari na Matatar Ɗangote.

Wannan mataki ya biyo bayan gano wasu tallace-tallace da ke yawo a kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin sanya hannun jari, duk da cewa babu wata takardar neman amincewa da aka gabatar ko aka amince da ita daga hukumar.

Hukumar ta bayyana cewa wasu kamfanonin dillancin hannayen jari da masu tallata saka hannun jari sun fara jawo hankalin mutane su yi rajista ko kuma su tanadi kuɗaɗe domin samun hannayen jarin matatar mai.

A sanarwar da ta fitar, SEC ta ce wannan aiki ba bisa ƙa’ida ba ne domin har yanzu ba a gabatar mata da bukatar yin IPO (Initial Public Offering) ba, balle ta amince da ita.

A cewar hukumar, irin waɗannan tallace-tallace na iya yaudarar masu zuba jari, su haifar da ruɗani a kasuwa, tare da lalata amincewar jama’a ga tsarin kasuwar hannayen jari na ƙasa.

Akan haka ne ta umarci duk masu ruwa da tsaki su dakatar da yaɗa sanarwa, fastoci, saƙonnin Imel da sauran kayan talla da ke da alaƙa da wannan tayin hannayen jari.

Haka kuma SEC ta umarci duk wani kamfani ko dillali da ya karɓi kuɗi daga masu saka hannun jari dangane da wannan tayin da ake zargi da shi da ya mayar da kuɗin cikin gaggawa.

Kazalika, hukumar ta yi gargadin cewa duk wanda ya ƙi bin umarnin nata, zai fuskanci hukunci bisa tanadin dokokin kasuwar hannayen jari na Nijeriya.

A baya dai attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana shirin fitar da wani kaso na hannayen jarin matatar mai ta Dangote domin jama’a su saya a shekarar 2026.

By Babaji

Leave a Reply