JIBWIS na shirin kai Sheikh Masussuka kotu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wata sabuwar takarda mai ɗauke da wasu zarge-zarge da gargaɗi daga Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Katsina ta jawo hankalin al’umma bayan da lauyoyin ƙungiyar suka aika da ita ga wani malamin addinin Musulunci mai suna Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka, mazaunin garin Dutsinma a jihar ta Katsina.

Takardar, wacce aka rubuta a ranar 15 ga Yuni, 2026, ta fito ne daga Imtiyaz Law Chambers, lauyoyin da ke wakiltar JIBWIS, inda suka bayyana damuwarsu kan irin wa’azuzzuka da koyarwar da malamin ke yi, waɗanda suka ce suna haifar da cece-kuce a tsakanin Musulmi tare da tayar da muhawara a kafafen sada zumunta.

A cikin takardar mai taken “Takardar Bayyana Damuwa, Gargaɗi da Buƙata” JIBWIS ta zargi Malam Yahya Masussuka da yin kalamai da suka shafi wasu fitattun littattafan Hadisi da kuma manyan malaman addinin Musulunci da suka rayu a lokuta daban-daban.

A cewar ƙungiyar, malamin ya yi amfani da kalamai masu zafi wajen sukar wasu daga cikin mashahuran littattafan Hadisi kamar Sahihul Bukhari da Sahih Muslim, inda ake zargin ya kira su da sunaye marasa kyau tare da yin bayanai da suka saɓa wa fahimtar mafi yawan malamai a tarihin Musulunci.

Takardar ta kuma yi zargin cewa malamin ya kan yi kalamai masu zafi kan wasu manyan malamai da suka haɗa da Imam Bukhari, Imam Muslim, Imam Tirmidhi, Imam Ahmad da kuma wasu malamai na wannan zamani, lamarin da JIBWIS ta ce na iya janyo rashin jituwa a tsakanin mabiyan addinin Musulunci.

Lauyoyin ƙungiyar sun bayyana cewa irin waɗannan kalamai ba kawai suna shafar mutuncin malamai ba ne, har ma suna iya haddasa rabuwar kai da rashin fahimta a tsakanin al’umma.

A wani ɓangare na takardar, JIBWIS ta bayyana cewa koyarwar da malamin ke yaɗawa tana da kamanceceniya da wasu ra’ayoyi masu tsattsauran ra’ayi da suka taɓa bayyana a tarihin Nijeriya, inda ta yi ishara da rikice-rikicen da suka shafi ƙungiyar Maitatsine a shekarun 1980 da kuma tashin hankalin Boko Haram a farkon shekarun 2000.

Sai dai ƙungiyar ba ta zargi malamin da aikata wani laifi na ta’addanci ba kai tsaye, amma ta bayyana cewa tana fargabar cewa irin salon wa’azin da yake yi na iya haifar da ruɗani da rashin fahimta idan ba a yi hattara ba.

Takardar ta ce: “Irin wannan salon wa’azi na iya haddasa rashin zaman lafiya, tayar da ƙura tsakanin mabambantan ra’ayoyi, da kuma jefa matasa cikin ruɗani dangane da fahimtar addininsu.”

JIBWIS ta kuma bayyana cewa a lokuta da dama an gayyaci malamin domin shiga tattaunawa da muhawara ta ilimi da wasu malamai domin warware saɓanin ra’ayoyin da ake samu, amma ta ce ya ƙi amsa irin waɗannan gayyata.

A cewar takardar, hanyoyin warware saɓanin fahimta a addini ya kamata su kasance cikin hikima, ilimi, mutunta juna da bin ƙa’idojin malamai, maimakon yin zafafan kalamai a kafafen sada zumunta.

Daga cikin buƙatun da JIBWIS ta gabatar wa malamin akwai ya fito fili ya janye wasu daga cikin kalaman da ya yi kan Hadisai da kuma manyan malaman Musulunci, tare da neman afuwa kan kalaman da ƙungiyar ta ce sun kasance na cin mutunci da zubar da ƙima.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙace shi da ya umurci masu kula da shafukansa na sada zumunta su cire wasu wa’azuzzuka da kalaman da ta bayyana a matsayin masu tayar da hankali da haddasa saɓani.

Takardar ta kuma yi nuni da cewa ƙungiyar tana da wasu bayanai da rikodin wa’azuzzukan malamin, waɗanda ta ce za ta iya miƙa wa hukumomin tsaro idan har ya kasa bin buƙatun da aka gabatar masa.

A ƙarshen takardar, lauyoyin JIBWIS sun bai wa Malam Yahya Masussuka wa’adin kwanaki 14 daga ranar da ya karɓi takardar domin ya amsa buƙatun da aka gabatar masa. Sun yi gargaɗin cewa idan ya gaza yin hakan, ƙungiyar za ta ɗauki matakan shari’a da ta ga sun dace domin kare abin da ta bayyana a matsayin muradun al’umma da zaman lafiya.

Lamarin ya haifar da muhawara a tsakanin mabambantan ra’ayoyin addini a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin cewa akwai buƙatar a magance irin waɗannan saɓanin fahimta ta hanyar tattaunawa da hujjojin ilimi, yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya kamata a kiyaye duk wani abu da zai iya haddasa rashin jituwa a tsakanin Musulmi.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga Malam Yahya Ibrahim Masussuka da ke nuna martaninsa kan takardar da JIBWIS ta aika masa.

Masu nazari kan harkokin addini sun bayyana cewa yadda za a tafiyar da wannan batu cikin hikima da bin doka zai taimaka wajen kauce wa duk wani rikici, tare da tabbatar da cewa muhawarar addini ta ci gaba da kasancewa cikin yanayi na ilimi, mutunta juna da zaman lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply