Gidauniyar Sidiya Charity ta ƙaddamar da shirin horar da mata sa’o’i don ƙarfafa tattalin arziƙi

Spread the love

A wani muhimmin mataki na inganta rayuwar al’umma, an ƙaddamar da Women Empowerment Training Initiative, wani shiri da Sidiya Charity Foundation ta assasa domin bai wa mata damar koyon sana’o’i da dabarun dogaro da kai, tare da ƙarfafa musu gwiwar zama masu cin gashin kansu a fannin tattalin arziki.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne cikin yanayi na farin ciki da fatan alheri, inda manyan baƙi, masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma da sauran masu goyon bayan ayyukan ci gaba suka halarta domin nuna goyon bayansu ga wannan gagarumin shiri.

Da take jawabi a wajen taron, Shugabar Gidauniyar, Hajiya Sadiya Sidi Said, ta bayyana cewa manufar shirin ita ce ba wa mata ilimi da ƙwarewar sana’o’i domin su samu damar dogaro da kansu, rage zaman banza, da kuma taimakawa iyalansu da al’ummarsu.

Ta jaddada cewa ci gaban kowace al’umma yana da alaƙa kai tsaye da irin damar da ake bai wa mata. Ta ce idan aka ba mace ilimi da sana’a, ba ita kaɗai ake gina ba, ana gina iyali ne, ana gina al’umma, kuma ana gina makomar ƙasa baki ɗaya.

Shirin zai haɗa da horaswa a fannoni daban-daban da suka haɗa da sana’o’in hannu, dabarun kasuwanci, koyar da yadda ake tafiyar da ƙananan sana’o’i, da kuma ba mahalarta shawarwari kan yadda za su bunƙasa harkokinsu cikin nasara.

Mahalarta taron sun yaba da wannan kyakkyawan yunƙuri, tare da bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na da matuƙar muhimmanci wajen rage talauci, samar da ayyukan yi, da ƙarfafa mata su zama ginshiƙan ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

A ƙarshe, Sidiya Charity Foundation ta yi kira ga gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane da su haɗa hannu wajen tallafawa irin waɗannan shirye-shiryen domin samar da al’umma mai ƙarfi, wadata da ci gaba mai ɗorewa.

“Lokacin da ka ba mace dama, ba mutum ɗaya ka canza ba; kana canza iyali, kana gina al’umma, kana kuma sauya makomar ƙasa..” Cewar shugaban kungiyar wato Haj. Sidiya

By Babaji