
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, ta umarci a gaggauta sakin Nura Idris, wato manomin da aka yi kuskuren kamawa bisa zargin hannun a ayyukan ta’addanci, bayan nazari da binciken da aka gudanar akansa sun nuna cewa shi wankakke ne daga hakan.
Daraktan Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi ne ya amince da sakin Idris bayan karɓar rahoton ababen da aka gano daga binciken da aka gudanar akansa, wanda a ciki babu wata hujja da ke alaƙanta shi da ‘yan ta’addar Boko Haram.
Haka kuma, Shugaban na DSS ya umarci a ba Idris Naira miliyan 3 a matsayin tallafi kuma a taimaka masa wajen fara sana’a domin sake gina rayuwarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, an gano Idris makiyayi kuma manomi ne ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, wanda aka kama shi a yankin Sulejan Jihar Neja a watan Yunin 2024 bisa zargin sa da hannu a ayyukan ta’addanci.
A cewar wani babban jami’in hukumar, bayan dogon nazari da aka gudanar akan al’amarin nasa, an gano cewa ba shi da wata alaƙa da ta’addanci don haka ne ma daraktan hukumar ya bayar da umarnin a gaggauta sakin nasa da kuma amince wa biyan sa diyyar.
Da yake karɓar kyautar, Idris ya yi godiya ga daraktan na DSS, yana mai cewa tallafin zai taimaka masa wajen sake gina rayuwarsa. Haka ma mahaifinsa, Yusuf Idris, wanda ya ƙara da cewa za a yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace.
