Harriet Tubman: Matar da ta girgiza tubalin bauta a Amurka

Spread the love

Bauta ita ce abu mafi kusa da jahannama da mutum zai iya rayuwa a cikinta – Harriet Tubman

Daga AISHA ASAS

Akwai matan da tarihi ya adana sunayensu sakamankon irin rawar da suka taka a sarauta. Akwai waɗada duniya ta nuna su saboda tarin dukiya. Akwai kuma waɗanda suka yi fice saboda ilimi ko shugabanci. Hakan ba yana nufin iya waɗanna ne tarihi ya tasakace ba, domin akwai waɗanda ba sarauta ce ta ɗaukaka su ba, kuma ba dukiya ce ta ba su suna ba, haka zalika ba mulki ba ne ya saka sunansu a a littafin tarihi ba.

Waɗannan mutane ba komai suka aikata ba da ya kai su wannan matsayi ba face tsaywa tsayin daka a lokacin da tsoro ya mamaye zukatan mutanensu, suka zama gata tare da sadaukar da rayuwarsu don ganin tsoron ya zama tarrihi a tsakanin al’ummarsu. Suka aikata abinda wasu ko a mafarki suka yi mafarkinsa sai sun tashi a tsorace. Wannan sadaukarwa ta rayuwarsu don mutanesu su rayu cikin kwanciyar hankali da mutunci ce ta sa tarihi bai baro su a baya ba.

Shafin Gimbiya na wannan makon ya waiwayi bauta da kuma irin gagarumar gudunmuwar da mata suka bayar wajen neman ‘yanci da kare bil’adama. Kuma idan aka bi wannan tarihi da ido na nazari, za a fahimci cewa gimbiyarmu ta wannan makon ba kawai suna ce a jerin masu gwagwarmaya ba, a maimakon haka ita ɗin ɗaya ce daga cikin kinshiƙan da suka gigiza tsarin da aka gina bautar ɗan adam.

Kada in cika ku da surutu, gimbiyar mu ta wannan mako ita ce jajirtacciyar mace da ta zama haske ga mutanenta a lokacin ƙangin bauta, wato Harriet Tubman.

An haife ta a cikin duhu na bauta, inda mutum ba shi da iko kan kansa, yayin da rayuwa take marar tabbas, iyali kuwa na kwana da zullumin rabuwa yau ko gobe ba tare da shiri ba. Tun tana ƙarama Harriet ta fuskanci abubuwan da yaran yanzu ba su sani ba, wato tsoro na kada a rabata da iyayenta, tsoron wanda ya kasance na yau da kullum, tsoro na kada a siyar da ita zuwa wani wurin da ba za ta sake ganin iyayenta ba. Tsoron rayuwar da ba ta da makoma.

Saidai a cikin wannan tsoron ne aka ƙyanƙyashe murya mai tambaya tare da tuhuwar abinda ake yi masu, me ya sa rayuwa za ta yi masu haka? Me ya sa rayuwa za ta keɓance su don farin cikin wasu?

Idan kun shirya, Aisha Asas ce ɗauke da tarihin Harriet Tubman. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Shin wacce ce Harriet Tubman?

An haifi Harriet Tubman da suna Araminta Ross a tsakanin shekarun 1820 zuwa 1822, a yankin Dorchester, Maryland a ƙasar Amurka. A lokacin, jihohin kudancin Amurka sun dogara sosai da bayi a fuskar aikace-aikace, musamman a gonakin auduga da taba, inda rayuwar baƙaƙen fata ke ƙarƙashin ikon masu mallakar gonakin.

Iyayenta Ben Ross da Harriet “Rit” Green, duk bayi ne. Wanda hakan na nufin tun daga haihuwa Harriet take mallakin wasu wadda ya hanata mallakar wani yanki na rayuwarta. Sunanta, aikinta, da makomarta duk suna hannun wani mutum.

Rayuwarta ta fara ne a irin wannan gida da a kullum ake cikin fargaban raba iyaye da ‘ya’yansu. Mahaifiyarta ta yi ƙoƙari matuƙa na ganin ta ba wa ‘ya’yanta kariya daga siyarwa, wannan na daga tushen jajircewarta, wato ta fara koyar darasi daga irin gwagwarmayar da mahaifiyarta ta yi don ganin ba a raba ta da su ba.

Yayin da ta fara girma, aka fara kaita aikin gida da na gonaki, ta soma da kula da yara ‘yan uwanta da ba su da ƙarfi, ta ɗauki kaya masu nauyi don ba su damar hutawa, ta zama wata kariya ga ‘yan uwa yara ba tare da la’akari da ƙurciyarta ko alaƙarta da yaran ba, wato alaƙa wadda ba ta jini ba. Duk tana wannan ne sakamakon zuciyarta ta daɗe da ba wa abinda ake yi masu matsayi da zalunci.

Yaya rayuwar bauta take a lokacin da Harriet take tasowa?

Rayuwar bauta a lokacin tasowar Harriet Tubman ba kawai aiki ne mai tsanani ba, tsari ne na mallakar ɗan adam gaba ɗaya. Bawa ba shi da ikon yanke shawara. Ba shi da ikon tafiya inda ya ga dama. Ba shi da ikon zaɓar abokai ko auren wadda yake so da sauransu.

A kowanne lokaci ana iya siyar da shi, ana iya raba shi da iyalansa ba tare da la’akari da yawan ‘ya’yansa ba. Haka kuma a kowane lokaci ana iya azabtar da shi komai tsufansa matuƙar hakan zai faranta ran mamallakin shi.

Harriet wadda ta buɗe ido a irin wannan rayuwa, ta ga yadda uwa ke kuka saboda an ɗauke mata ‘ya’ynata. Ta ga yadda maza ke shan bulala saboda ƙananan kura-kurai. Ta ga yadda tsoro ke zama kamar wucewar isa a rayuwar yau da kullum. A hankali wata tambaya mai tasiri a yanzu ta dasu a zuciyarta; Shin iyakan indan rayuwarsu ya kamata ta tsaya kenan?

Ko akwai raunin da ta samu a lokacin ƙurciya da ya sauya rayuwarta?

A lokacin da take kusan shekaru 13, wani lamari ya faru da ya canza rayuwarta baki ɗaya. Wani bawa ne ya yi ƙoƙarin tserewa, sai mai kula da bayin ya ɗauki wani ƙarfe mai nauyi da aniyar jefa masa shi don hana shi ƙudurinshi. Amma a bisa tsautsayi ƙarfen ya kaucewa inda aka jefa shi ya faɗa bisa kan Harriet.

Take ta faɗi jini na zuba har an yi tsamanin ma rai ya yi halinsa. Saidai bayan doguwar jinya, ta tsira da ranta, amma tun daga lokacin ta samu raunin da ke saka ta fama da matsanancin ciwon kai wanda wasu lokutan idan ya taso har suma take yi. Ciwon kuwa na zuwa ne ba tare da gargaɗi ba, wanda hakan ke sa wasu lokuta idan tana tsaye sai ta faɗi ba shiri, wani lokacin ke kai ta da suma har sai an kwashe ta saboda tsananin ciwon. Wani lokacin kuwa tana barci mai tsanani da har a farko ake ganinsa a matsayin mutuwa.

Saidai wani abun da zai baka mamaki shi ne, yadda ta ɗauki rauninta ta mayar da shi ƙarfi, ta hanyar mayar da akalar ciwonta zuwa baiwa. Domin takan faɗa wannan hali da take shiga wata hanya ce da ake yi mata wahayi, wanda ta yi imanin yana nuna mata hanyar mafita ga halin da suke ciki.

Shin hakan na nufin ita ɗin ma’abuciya riƙo da addini ce?

Harriet Tubman ta kasance ma’abuciya riƙo da addinin da ta tarar da iyayenta kansa.  Don haka ta gina rayuwarta a kan imani mai ƙarfi na cewa, Allah na tare da waɗanda ake zalunta. Ba ta kallon kanta a matsayin mace mai ƙarfin zuciya ko jajircewa, maimakon haka tana kallon kanta a matsayin mai bin jagorancin ubangijinta, wanda ta danganta ƙarfin da take da shi daga wurin sa. A duk lokacin da ta fuskanci wani hatsari, ba ta dogaro da ƙarfin jikinta kaɗai, takan dogara da imaninta wanda ya tabbatar mata za ya nuna mata hanya. Wannan kuwa shi ne makamin da ta ya cimma duk wata nasara da ta samu.

Ko Harriet ta yi aure? kuma wacce rawa auren nata ya taka a tafiyar da ta yi ta rayuwa?

Tarihi ya tabbatar da uaren Harriet Tubman da wanda ake cewa John Tubman a shekarar 1844. Auren kuwa ya ƙara buɗe mata ido da kuma ƙarin kwarin gwiwa kan neman ‘yanci, ba kuwa don komai ba face kasancewar mijin nata mai ‘yanci duk da kasancewarsa baƙar fata. Harriet Tubman ta ga bambanci tsakanin rayuwar ‘yanci da rayuwar bauta ta kai tsaye. Ta kuma ɗan ɗanɗani zaƙin da ke tare da ‘yancin kai, wanda ya ƙara mata fata da burin samun haka ga kanta da kuma sauran mutanen da ke cikinsa.

Saidai a lokacin da ta soma shirin cika burinta na tserewa, ba ta samu goyon bayan mijinta John ba, a cewarsa hakan na da hatsari mai yawa gare shi, kuma ya nuna mata hatsarin hakan mai yawa ne. (Duk da mun faɗa mijin nata yana da ‘yanci hakan ba yana nufin ita ta zama ‘yantatta ba, kuma shi karan kansa akwai wasu dokoki da suke kansa duk da cewa an ba shi ikon kansa).

Duk da irin yadda mijin nata ya sanyaya mata gwiwa hakan bai rage ƙudurin nata ba, domin a ganinta rayuwa cikin sarƙoƙin bauta shi ne mafi hatsari.

Bari mu je ga tambaya mai muhimanci wato me ya sa ta yanke shawarar tserewa?

A shekarar 1849, bayan mutuwar mai mallakar ta, Harriet ta ji raɗe-raɗen yiwar siyar da ita wani wurin a hannun wani daban. Hakan ya tayar mata da hankali matuƙa, domin ba komai hakan ke nufi ba face rabuwa da iyalanta da duk wani da ta saba da shi, ko ince rabuwa da rayuwarta gaba ɗaya zuwa wata rayuwar da ba ta san me ke jiranta ba.

Don haka ba ta bari maganganun mijinta suka yi tasiri ba, ta bi dare, ba tare da sanin inda za ta dosa ba, ba tare da wata kariya ba, kuma ba tare da tabbacin abinda yake gaba ba, ta dunfari zaɓin mutuwa ko rayuwa ba tare da tabbaci ba. Ta zaɓi shiga rashin sani da ta jira sanin da zai jefa rayuwarta a wani sabon rashin adalci da zalunci. Babu guzurin da ta yi mai ƙwari da ya kai ƙudirin da take da shi na ta tsallake rijya, har ta samu damar dawowa wata rana ta ceci masu rauni da ba za su iya yin abinda ta yi ba na daga al’ummarta.

Ko wannan hukuncin ya kaita ga ‘yanci a karon farko?

Na san mai wannan karatun dai ba zai yi tsamanin wannan tafiyar ta zo da sauƙi ba, domin ta yi tafiya cikin dare cike da rashin tabacin abinda za ta risaka a gaba. Ta yi ɓuya ba iyaka don gujewa masu farauta na daga inda ta fito da kuma inda za ta. Ta bi dazuka don samun maɓuya yayin da ta kauce wa hanyoyi marar hatsari, ba wani taimako sai amfani da taurari da take yi don hasashen inda ya kamata ta bi.

Bayan wahala mai tsanani, Harriet ta isa Philadelphia. A nan ne a karon farko ta fara jin abin da ake kira mallakar kai, ta jiwo ƙarmshin ‘yanci ta kowane ɓangare.

Me ya sa ta ta koma inda aka bautar da ita bayan ta samu ‘yanci?

Da wannan tamyar za mu yi bankwana, inda da yardar Mai Duka mako mai zuwa za mu fara da ita kafin sauran tambayoyin su biyo baya.

Sannunku masu karatunmu da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja

By ukarofi

Leave a Reply