Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki ƙarin malamai na makaratun firamare da na sakandire 2,185 da gwamna Raɗɗa ya ce wani cigaba ne aka samu a ƙoƙarin gwamnatin sa na sake gina harkar Ilimi a jihar.
Gwamnan wanda ya ƙaddamar da bada takardar kama aiki ga malaman a Katsina ya bayyana ilimi a matsayin wani makami da zai canza rayuwar al’ummar” Zuba jari a harkar Ilimi tamkar zuba jari a makomar Jihar ne.
Dikko ya ce a 2023 shekarar da suka hau kujerar mulki sun ɗauki malamai na firamare da sakandire 7,323 da malaman kiwon lafiya 1800 da aka dauka aiki a ƙanana da manyan asibitocin jihar.
Gwamnan ya kuma yi bayani kan wasu matakai da gwamnati ta ɗauka na inganta ilimi a jihar waɗanda suka haɗa da gina makaratun firamare da na sakandire guda 49 da makarantu na musamman guda uku.
Haka kuma gwamnatin jihar ta yi gyaran makarantun gida 340 tare da samar masu da kayan karatu,biyan kuɗin jarabawa na shiga manyan makarantu da bayar da horo ga malaman makarantun jihar.
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa malaman makarantu 25000 suka sami horo a lokuta daban daban domin ƙara ƙwarewa a harkar koyarwa da biyan alawus na 30,000 ga malaman makarantu da ke koyarwa a karkara da kuma tallafawa da baburan hawa mai amfani da hasken rana ga malaman da ke koyarwa a ƙauyukan da hanyar su bata da kyau.
Ya gargaɗi sabbin malaman da aka ɗauka da su gudanar da aikin su bisa amana, gaskiya da su guji makara ko rashin zuwa makaranta.
Tun farkon jawabin sa kwamishinan Ilimi a Jihar Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya sanar da cewa daga 2023 zuwa yau gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ɗauki malaman makarantu 9000.
Sabbin malaman da aka ɗauka aiki za su zama a ƙananan hukumomin da suka fito domin sauƙaƙa malaman.
