Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Masana a fannin sadarwa, talla da aikin jarida sun buƙaci a inganta harkokin tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai domin bunƙasa sana’ar da kuma kawar da matsalolin da ke addabarta.
An bayyana hakan ne yayin taron Advertising Practitioners Association of Kano (APAK) da aka gudanar na kwanaki uku a Kano.
Masu jawabi sun tattauna hanyoyin da za a inganta ingancin tallace-tallace, daidaita amfani da harshen Hausa, da kuma tabbatar da ƙa’idojin aikin talla tsakanin Arewa da Kudancin Nijeriya.
Taron ya samu halartar masana daga jami’o’i, kamfanonin talla da kafafen yaɗa labarai daban-daban.
Daga cikin waɗanda suka gabatar da muhimman jawabai akwai Farfesa Umar Fari, Farfesa Sule Yau Sule, Farfesa Abdullahi Uba, Dakta Bala Muhammad da Dakta Dukawa, dukkansu daga Jami’ar Bayero Kano. Haka kuma akwai wakilai daga kamfanonin Aspira, BRC da sauran manyan kamfanoni.
Sai dai bayan kammala taron, wasu mahalarta sun bayyana rashin jin daɗinsu kan wasu matsalolin da suka ce sun fuskanta. Sun yi korafin matsalar sautin lasifika a dakin taro, da rashin wadataccen abinci a ranar ƙarshe, inda suka ce daga karin kumallo har zuwa ƙarshen taro ba a sake ba su wani abin ci ba.
Wasu kuma sun yi zargin rashin adalci wajen rabon takardun shaidar halarta (Certificate), inda suka ce an buƙaci wasu su biya kuɗi kafin su karɓi takardarsu, alhali wasu sun samu ba tare da biyan kuɗi ba.
ƙoƙarin jin ta bakin masu shirya taron domin jin martaninsu bai yi nasara ba.
