Gwamnatin Nasarawa ta amince da ɗaukar malaman firamare 1000 aiki

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Kimanin masu neman aiki 10,000 ne suka fafata domin samun guraben aikin malaman makarantar firamare 1,000 da gwamnatin jihar Nasarawa ta amince da su ƙarƙashin wani tsari na musamman na ƙauyuka kamar yadda jami’in gwamnatin ya bayyana a ranar Litinin na mako da ake ciki a Lafia.

Mataimaki na musamman ga gwamna Abdullahi Sule kan harkokin jama’a hon. Peter Ahemba wanda ya wakilci gwamnan a wani taron manema labarai na kowanne watanni biyu da aka gudanar a sakatareiyar ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa, NUJ ta jihar Nasarawa dake Lafia babban birnin jihar ne ya bayyana hakan kan wani tsari na musamman na ɗaukar ma’aikata da hukumar Ilimi ta SUBEB ta gudanar.

Ahemba yace gwamnatin jihar ta amince ɗaukar malaman firamare 1,000 ne musamman domin magance matsalar ƙarancin malami a yankunan ƙauyuka yana mai jaddada cewa duk wanda ya samu nasara za a tura shi kai tsaye zuwa makarantun ƙauyuka.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta wuce ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata na yau da kullum kuma ta bai wa wani kamfanin ba da shawara mai zaman kansa aikin domin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin.

A cewar bayanin da aka bayar an samu yawan masu neman aikin da yawa amma kashi kaɗan ne kawai suka ci jarabawar.

Ko da yake har yanzu ba a fitar da cikakken rabon makin jarabawar ba amma sama da waɗanda suka fafatan 10,000 ne suka nemi guraben aikin 1,000 da ake dasun.

Ahemba ya tabbatar da cewa tsarin zai kasance cikin gaskiya da bai wa wanda ya cancanta yana mai cewa manufar tura malaman zuwa ƙauyuka ita ce a rufe giɓin malaman da ke cikin al’ummomin da ke da wuya a shiga a faɗin jihar inda ya kuma yi amfani da samar ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnatin ta jihar ta buƙaci masu neman aikin da su jira sabon sanarwa daga hukumar SUBEB ɗin da kamfanin ba da shawara kan mataki na gaba na wannan aikin kwasan malaman firamare ɗin da gwamnatin ke yi a yanzu.

By ukarofi