Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Birnin Kebbi, a ranar Laraba 8 ga Yulin 2026, ta amince da buƙatar da Samir Salihu Felande ya gabatar na ba shi izinin shigar da ƙarin takardu daga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) a ƙarar da ya shigar kan sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da ta ce ta yi na ƙananan hukumomin Argungu/Augie.
Wannan hukunci ya zama wani muhimmin ci gaba a shari’ar da ake yi tsakanin Felande da ɗan takarar APC, Umar Hassan Augie.
Da ta ke zantawa da manema labarai bayan kammala zaman kotun, lauyar mai ƙara, Munirat O. Yahaya, ta bayyana cewa a zaman da ya gabata sun nemi kotu ta ba su damar gabatar da wasu takardu da suka samo daga INEC, waɗanda suka yi imanin za su taimaka wajen yanke hukunci cikin adalci.
Ta ce INEC ta ƙalubalanci buƙatar ta hanyar gabatar da takardar ƙin amincewa, tana roƙon kotun da kada ta amince da ita, sai dai bayan sauraron hujjojin ɓangarorin da ke shari’ar, kotun ta yanke hukunci tare da amincewa da buƙatar mai ƙara.
Munirat Yahaya ta ƙara da cewa bayan wannan hukumcin kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar Laraba, 15 ga Yulin 2026, domin fara sauraron muhimman hujjojin ɓangarorin.
Shari’ar ta samo asali ne daga ƙalubalantar da Samir Salihu Felande shigar kan ayyana Umar Hassan Augie a matsayin ɗan takarar APC na mazaɓar Tarayya ta Argungu/Augie. Felande na iƙirarin cewa ba a gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani ba kafin a ayyana Turakin Augie a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
