Na taɓa faɗa wa ‘yan bindiga su halaka ‘yan uwana akan na ba su kuɗin fansa, inji Gwamnan Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba ko biyan su kuɗaɗen fansa don saboda sun yi garkuwa da mutane.

Dauda Lawal ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a taron manema labarai a game da al’amarin ‘yan sandan jihohi, ranar Alhamis.

A cewarsa, a shekarar 2019, an sace ‘yan uwansa maza biyu, inda ‘yan bindigar da ke da alhakin haka suka nemi a biya Naira miliyan 300 a matsayin kuɗin fansarsu.

Ya ce, a madadin haka sai ya faɗa musu cewa su halaka ‘yan uwan nasa idan sun ga dama saboda shi ba zai biya kuɗin fansa ba.

Gwamnan ya bayyana cewa, biyan kuɗin fansa na ƙara ƙarfafa wa masu aikata laifuka, yana mai jaddada cewa bai yarda da tattaunawa ko biyan kuɗi ga masu garkuwa da mutane ba.

Haka kuma, ya ce gwamnati na cigaba da ɗaukar matakan da suka dace domin yaƙi da matsalar garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Kazalika, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tallafa wa ‘yan sandan jihohi domin yaƙar masu aikata miyagun laifuka a Zamfara.

By Babaji