Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani rahoto ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu amincewar ciyo rancen da ya kai dala biliyan 11.4 daga Bankin Duniya cikin shekaru uku na farko da ta yi kan mulki, lamarin da ya kusantar da ita ga zarce adadin dala biliyan 14.59 da aka amince wa Nijeriya a zamanin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na tsawon shekaru takwas.
Binciken bayanan Bankin Duniya ya nuna cewa daga watan Yunin 2023 zuwa Yunin 2026, Nijeriya ta samu amincewar rancen da ya kai dala biliyan 11.4, wanda ya kai kusan kashi 78 cikin 100 na jimillar kuɗaɗen da aka amince wa ƙasar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023 a mulkin Buhari.
Da wannan ci gaba, gwamnatin Tinubu na buƙatar kusan dala biliyan 3.19 kacal domin ta zarce tarihin da aka kafa a gwamnatin da ta gabata.
Sai dai, rahoton ya nuna cewa daga cikin kuɗaɗen da aka amince da su, dala biliyan 2.32 ne kawai aka fitar zuwa yanzu, yayin da sama da dala biliyan 8.4 ke jiran a sake su yayin da ayyukan da aka ware kuɗaɗen domin su ke cika matakan aiwatarwa da aka gindaya.
An ware yawancin rancen ne domin tallafa wa muhimman fannoni da suka haɗa da gyaran tattalin arziki, wutar lantarki, noma, ilimi, kiwon lafiya, inganta ababen more rayuwa na fasahar zamani, bunƙasa hada-hadar kuɗi da kuma shirye-shiryen kariyar zamantakewa.
ɗaya daga cikin manyan rancen da aka amince da shi shi ne na dala biliyan 2.25 a watan Yunin 2024, wanda Bankin Duniya ya ware domin tallafa wa shirin gyaran tattalin arzikin Nijeriya.
A cewar Bankin Duniya, an tsara wannan tallafi ne domin ƙarfafa zaman lafiyar tattalin arziki, bunƙasa tattara kuɗaɗen shiga cikin gida da kuma kare talakawa da masu rauni yayin aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.
Haka kuma, a watan Yunin 2026, Bankin Duniya ya amince da dala biliyan 1.25 domin aiwatar da shirin Nigeria Actions for Investment and Jobs Acceleration, wanda ke da nufin bunƙasa masu zuba jari masu zaman kansu, samar da ayyukan yi, faɗaɗa samun makamashi, inganta ababen more rayuwa na fasahar zamani da kuma haɓaka yawan amfanin gona.
Sauran rancen da aka amince da su sun haɗa da shirye-shiryen makamashi mai sabuntawa, bunƙasa noma, kiwon lafiya, ilimi, fasahar zamani, inganta damar samun ayyukan kuɗi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin mata.
Da yake tsokaci kan ƙaruwa a yawan rancen Bankin Duniya da Nijeriya ke samu, masanin tattalin arziki da ke Legas, Adewale Abimbola, ya bayyana cewa karɓar bashi daga cibiyoyin kuɗi na duniya ba matsala ba ne matuƙar ana amfani da kuɗin wajen ayyukan da za su haifar da ci gaba.
Ya ce, “Karɓar bashi ba laifi ba ne. Abu mafi muhimmanci shi ne yadda ake amfani da shi. Idan rancen yana da sauƙin biya kuma an ware shi domin ayyukan da za su samar da kuɗaɗen shiga a nan gaba, ba na ganin akwai matsala.”
Shi kuwa masanin tattalin arzikin ci gaba, Dakta Aliyu Ilias, ya yi gargaɗin cewa yawan bashin na iya zama nauyi idan ba a kula da yadda ake tafiyar da shi ba. Ya ce, ya kamata gwamnati ta tabbatar cewa kuɗaɗen bashin suna haifar da ingantattun ayyukan gwamnati, samar da ayyukan yi da kuma ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
