Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Makarantar Alƙur’ani mai girma da Islamiyya ta Mu’assasa Ma’ahad Ishaƙ Rabiu, ƙarƙashin jagorancin Gwani Imam Yahaya Umar Baba, ta gudanar da gagarumar walimar saukar Alƙur’ani karo na biyar a tarihinta.
A cewar shugaban makarantar, ɗalibai 100 ne suka haddace Alƙur’ani gaba ɗaya, yayin da wasu 70 suka kammala karatun biye da Alƙur’ani mai girma.
Ya bayyana hakan ne yayin walimar da aka gudanar a harabar makarantar da ke unguwar Yahaya Gusau a Kano a ƙarshen makon da ya gabata.
Gwani Imam Yahaya Umar Baba ya ce baya ga koyar da Alƙur’ani, makarantar tana koyar da littattafan addini da harshen Larabci tare da mai da hankali wajen tarbiyyar ɗalibai da gina musu tsoron Allah.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni da hukumomi su yi koyi da marigayi Khalifa Ishaƙ Rabiu wajen kafa makarantu da tallafa wa harkar ilimi domin amfanin al’umma.
A ƙarshe, ya buƙaci iyaye da malamai su ci gaba da koya wa yara muhimmancin girmama ilimi, malamai da littattafai, musamman Alƙur’ani mai girma.
