Da Ɗumi-Ɗumi: Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da sako ɗalibai da malaman Oyo da aka sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da ceto baki ɗaya malamai da ɗalibai makarantar Orire ta Ogbomoso da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo.

Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga me ya bayyana haka ta kafar X a ranar Juma’a.

Ya ce, hukumomin tsaro sun yi nasara ceto dukkanin waɗanda al’amarin ya shafa, lamarin da yak awo ƙarshen rashin tabbas game da halin awon-gaba da su.

Saidai, Fadar ba ta bayar da karin bayani akan yadda aka ƙaddamar da atisayen ceto mutanen ba.

Haka kuma, hukumomin tsaro ba su fitar da wani saƙo na musamman akan al’amarin ba yayin haɗa wannan rahoto.

An ga yadda wata malama, wadda ɗaya ce daga cikin waɗanda aka sacen, tana yi wa Shugaba Bola Tinubu godiya akan ceto su da aka yi.

By Babaji