Idan aka halaka ni, Amurka za ta shafe ku a doron ƙasa – Trump ga Iran bayan jana’izar Ali Khamenei

Spread the love

Shugaba Donald Trump na Amurka ya gargaɗi Iran da cewa za ta fuskanci mummunan martanin sojin ƙasarsa matuƙar ta yi yunƙurin halaka shi ko kai masa wani hari.

A wani saƙo da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social, Trump ya bayyana cewa ya riga ya bayar da umarnin da suka dace ga hukumomin tsaro, yana mai cewa Amurka ta shirya tsaf domin mayar da martani cikin gaggawa idan aka aiwatar da wata barazana a kansa.

Ya yi ikirarin cewa dubban makamai masu linzami suna cikin shiri, yana mai cewa duk wani yunkurin kai masa hari zai jawo farmakin da zai yi wa Iran mummunar illa.

Trump ya kuma ce, ƙarfin sojojin Amurka ya isa ya kai hare-hare masu faɗi a sassan Iran idan aka tilasta musu yin hakan.

Wannan gargaɗi na Trump ya zo ne bayan wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa jami’an leƙen asirin Isra’ila sun gano abin da suka bayyana a matsayin wani sabon shirin da ake zargin Iran na yi domin kashe tsohon shugaban na Amurka.

Har ila yau, an ga wasu hotuna da kalamai masu nuna adawa da Trump yayin jana’izar Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da ya ƙara tayar da ce-ce-ku-ce.

Sai dai gwamnatin Iran ta ci gaba da musanta duk wani zargi da ke cewa tana da wata manufa ko shirin kashe Donald Trump.

By ukarofi