2027: Tinubu zai samu gagarumar nasara a arewa kan sake ɗaukar Shettima a matsayin abokin tafiya, inji Iliyasu Kwankwaso

Spread the love

Sake ɗaukar Sanata Kashim Shettima da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin maitaimakinsa a zaɓen shekarar 2027 ya tabbatar wa Jam’iyyar APC sake samun gagarumar nasara a Arewacin Nijeriya domin kusan kowa zai sake zaɓen su domin cigaba da ayyukan raya ƙasa kasa, kamar yadda Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa na Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are ya bayyana.

Ya ce, wannan abin murna ne ga yankin Arewa baki ɗaya musamman ganin yadda shugaban ya fifita tafiyar Musulmi da Musulmi.

Shugaba Tinubu ya miƙa form ɗinsa na sake tsayawa takarar Shugaban Kasa ga babban Kwamitin Jam’iyyar APC a inda ya bayyana Kashim Shettima a matsayin Maitaimakin sa a zaben shekarar 2027 a Abuja. A fadar Kwankwaso wannan matakin ya jefa makiyan Shugaba Tinubu cikin rudani.

Shugaba Tinubu ya sanar da Kashim Shettima a matsayin Maitaimakin sa ta bakin Ibrahim Masari Maitaimaki na musamman ga Shugaba Tinubu kan Harkokin Siyasa yayin mika fom din Shettima yayi wani taro da manyan Shugabanin Jam’iyyar APC suka halarta a Abuja. Wanna babban al’amari ne ga cigaban kasa.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya sanar da murnar na da fatan alheri a samarwan da ya isar ga manema Labarai inda ya kara da cewa Maitaimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima na cikin sahun gaba wajen nasarorin da gwamnati ke samu.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya cigaba da cewa Maitaimakin Shugaban Kasa yayi amfani da basira wajen hada kawunan yan Arewa duk da wasu tsirarun yan adawa suna kokarin kawo rudani.

” Mun gan yanda Kashim Shettima yake ta kokarin hada kawunan yan Arewa dana Yan Najeriya kuma mun gan irin wakilci nagari da yake yi duk lokacin daya wakilci Shugaban Kasa a Kasashen Duniya.

Kwankwaso ya tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa Jam’iyyar APC zata sami nasara mai rijanyen gaske a Arewacin Najeriya saboda sake daukan Kashim Shettima a matsayin Maitaimakin sa.

Kuma Jam’iyyar APC zatayi nasara a zaɓukan gwamnoni da sauran kujerun da za’a yi takarar su .

By Babaji

Leave a Reply