Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Alhaji Mohammed Dandare Kyangakwai ya sanar da ficewar sa daga Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi tare da sanar da komawa Jam’iyyar ADC ta adawa.
Ya yi wannan bayanin ne a garin Argungu yayin wata ziyara da ya kai wa ɗan takarar kujerar Sanata a gundumar Kebbi ta Arewa Alhaji Ibrahim Muhammad Mera.
Ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan ganawa da magoya bayan sa da kuma abokan hulɗar sa na al’amurran yau da kullum.
Ya kuma yi kira ga dukkan magoya bayan sa da ma kowa ya koma mazaɓar sa ya yi rajista da Jam’iyyar ADC daga tushe.
Ya ƙara da cewa ya zama wajibi ga duk wanda ke nufin alkhairi ga wannan ƙasar ya bayar da nasa gudummawa wajen ganin an sami canjin gwamnati.
