Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cikakken ƙwarin gwiwarsa cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta samu nasara a babban zaɓen shekarar 2027.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen “Tinubu-Dikko Again 2027” a birnin Katsina.
Ofishin yaƙin neman zaɓen, wanda tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shema ya kafa, domin haɗa kai da daidaita goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa yana da cikakken tabbacin APC za ta ci gaba da riƙe mulki a shekarar 2027, sakamakon ƙarfin tsarin jam’iyyar daga matakin ƙasa har zuwa tushe da kuma irin goyon bayan da take samu daga al’ummar Jihar Katsina.
Ya ce kwamitin yaƙin neman zaɓen, wadda ta tanadi tsari a dukkan ƙananan hukumomi 34, gundumomi da rumfunan zaɓe, za ta ƙara ƙarfafa wayar da kan mata, matasa da sauran magoya bayan jam’iyyar.
Gwamnan ya ƙara da cewa APC za ta bayyana cikakken shirinta na yaƙin neman zaɓe a lokacin da ya dace, tare da fafatawa da jam’iyyun adawa lokacin da hukumar zaɓe ta amince da fara kamfen.
“Ba ni da wata shakka, ba ni da tsoro, kuma ba ni da wata fargaba game da nasararmu a zaɓe mai zuwa,” in ji Gwamna Raɗɗa.
Ya danganta wannan ƙwarin gwiwa da taimakon Allah, goyon bayan shugabannin jam’iyya da kuma amincewar talakawan jihar da ayyukan gwamnatinsa.
Gwamna Raɗɗa ya yabawa tsohon Gwamna Ibrahim Shema bisa kafa wannan dandali na yaƙin neman zaɓe, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa APC a fagen siyasa a Jihar Katsina.
A nasa jawabin, tsohon Gwamna Ibrahim Shema ya buƙaci dukkan ‘ya’yan APC su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa baya.
