
An gudanar da allurar Rigakafin Ƙwayar Cutar Tetanos ga adadin yara sama da 90,000 na ɗaukacin Ƙaramar Hukumar Bichi, inda kuma ƙaramar hukumar ta kasance a cikin ƙananan hukumomi 10 da suka ciri tutar gudanar da wannan muhimmin aikin yadda ya kamata a faɗin jihar Kano.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta raba wa manema labarai.
Ta bayyana cewa, Shugaban Sashen Lafiya a Matakin Farko, Alhaji Kabir Abubakar Gwarzo, wanda ya samu wakilcin Jami’in Gudanar da Allurar Rigakafi na ƙaramar hukumar, Malam Mahmud Garba ya ce, Bichi na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 18 a cikin Jihar Kano da aka gudanar da wannan rigakafin ta hanyar samun yara mata a makarantu da ƙofar gidan dagatai da kuma masu unguwannin yankin, waɗanda shekarun su suka kama daga 15-49.
Kazalika, Jami’in Kula da Harkar Sadarwa da Walwala na Sashen Lafiya dake Bichi, Malam Nura Ibrahim Abubakar, ya ƙara da cewa, Kano tana daga cikin jihohi 4 a Nijeriya da suke fama da Tetenos da ciwon mashako.
A hannu guda kuma ya koka bisa yadda wasu daga cikin al’umma suke ƙaurace wa asibitoci domin karɓar allurar rigakafi domin inganta kiwon lafiyarsu.
Du ba da haka, Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Malam Zakari Sani, ya bayyana Cutar Tetanos (MNTE) tana da matuƙar hatsari bisa la’akari da yawan mutuwar da mata suke yi wajen haihuwa sanadinta, kuma ƙwayar cutar bakteriya ce da ake samunta ta hanyar kura da ƙasa.
“Kowa ya sani ba za a raba ɗan’adam da ƙasa ba (ƙasa wadda muke takawa), musamman yankunanan karkara, ita kuma Cutar Tetenos MNTE (Maternal and Neonatal Tetanus Elimination) da zarar mutum ya samu wata kafa ta rauni ko ciwo iska take aika ta cikin jikinsa, muddin ba a yi masa rigakafinta ba.
Shi ya sa idan ba a yi wa mace ba da zarar ta zo gargarar haihuwa idan ta samu rauni Tetenos na iya shigarta abin da ta haifa ma kan iya mutuwa, sannan Cutar Tetanos ga mai haihuwa ita ma wani nau’i ce a ɓangaren jijjiga, amma idan aka yi wa mace rigakafin wannan cuta sau 5 kamar yadda yake yana ba da kariya ne tsawon rayuwa.” Malam Zakari Sani.
A ɓangaren Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata, wanda ya samu wakilcin Sakataren Mulki na yankin, Alhaji Anas Muhammad Abdullahi, ya ja hankalin dukkan masu alhakin gudanar da ayyukan rigakafi a yankin, a kan su riƙa gudanar da aikin a cikin kwarewa da nutsuwa da kiyaye doka da oda wajen sauke nauyin dake wuyansu. Kana ya jaddada za su yi iya yinsu don samun nasarar inganta lafiyar al’ummarsu.
A gaɓar ƙarshe, an samu ingantattun shawarwari daga masu ruwa da tsaki na aikin, musamman ta yadda za a faɗaɗa wayar da kan jama’a ta fuskar ƙiƙirar sabbin hanyoyi da dabarun isar da saƙonni, tare da assasa jin daɗi da walwalar masu riƙe da masarautu dangane da wannan gagarumin aikin da suka fi kowa taka rawar gani a yayin gudanarwa.
Zaman ya ƙunshi; Shugaban Kansilolin yankin Sifika, Wakilin Hakimin Bichi Galadiman Kano, STF wakilin Kwamishinan Lafiya na jiha, Focal Person LGACEF, Sakataren Iimi na ƙaramar hukumar, WDC ta Bichi, FOMWAN Amira, Kwamandan Hisba, Limanin Bichi, dagatai da masu unguwanni da sauransu.




