An haramta wa’azi da talla a motocin kasuwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Doka za ta fara cin tarar N50,000 ga masu talla ko wa’azi acikin motocin kasuwa yayin Gwamnatin Tarayya ke ƙoƙarin tabbatar da dokar gyare-gyare a dokokin tuƙi a Nijeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawa ta tabbatar da ƙudirin gyaran Dokar Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta 2026, wanda ke neman a ƙarfafa ayyukan hukumar da haramta wasu ayyuka da ka iya ɗauke hankalin direba yayin da yake tuƙi.

A yanzu hakan na jiran amincewar shugaban ƙasa domin ganin an aiwatar da dokar a ƙarƙashin kulawar FRSC.

Idan aka sanya mata hannu a dokance, dokar za kuma ta shar’anta biyan N50,000 ko zaman kurkuku na wata shida ko kuma duka biyun ga masu ababen hawan da suka bijire wa jami’an FRSC yayin da suke bincike.

An ɗauki wannan mataki ne yayin nazari mai girma akan harkokin FRSC da kuma ƙoƙarin biyayya ga dokokin tuƙi, rage yawan haɗurra da inganta bayar da kariya a titinan Nijeriya ta hukunta masu aikata laifukan da suka shafi tuƙi.

By Babaji

Leave a Reply