Tinubu ya nemi majalisa ta sake nazari kan ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Wakilai ta sake nazari tare da ƙara himma wajen duba ƙudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya domin samar da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, a wani sabon yunƙuri na gwamnatin tarayya na sake fasalin tsarin tsaron ƙasar.

A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 15 ga Yuni da shugaban ya aika wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya buƙaci majalisar ta gaggauta duba ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin da zai ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi.

A cewar shugaban ƙasar, ƙudirin zai samar da ginshiƙin doka a kundin tsarin mulki domin bai wa jihohi damar kafa rundunonin ‘yan sanda nasu, tare da ci gaba da wanzuwar rundunar ‘yan sandan tarayya.

Tinubu ya bayyana cewa ƙudirin na daga cikin muhimman tsare-tsaren gwamnatinsa na sake fasalin tsarin tsaron Nijeriya domin magance matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar nan.

“Wannan ƙudiri zai samar da hanyar da kundin tsarin mulki ya tanada domin kafa rundunonin ‘yan sandan jihohi,” inji shugaban.

Ya ƙara da cewa ƙudirin ya ginu ne kan aikin da Majalisar Wakilai ta riga ta gudanar kan batun, tare da ƙara wasu matakan kariya domin tabbatar da cewa tsarin ‘yan sanda na tarayya da na jihohi zai yi aiki yadda ya kamata.

“Wannan ƙudiri ya ginu ne kan gagarumin aikin da Majalisar Wakilai ta riga ta yi a wannan fanni, tare da ƙarfafa matakan kariya domin tabbatar da cewa an kafa tsarin ‘yan sanda biyu da zai taimaka wajen tunkarar ƙalubalen tsaron da Nijeriya ke fuskanta cikin gaggawa,” inji Tinubu.

Shugaban ya ce ƙudirin wani muhimmin ɓangare ne na dabarun gwamnatinsa na sake fasalin tsaron Nijeriya domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma yadda ya kamata.

Idan aka amince da ƙudirin, zai kawo ƙarshen tsarin da ya bai wa gwamnatin tarayya kaɗai ikon gudanar da aikin ‘yan sanda, inda kundin tsarin mulki zai ba gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi damar mallakar rundunonin ‘yan sanda da doka ta amince da su.

A halin yanzu, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ce kaɗai ke da ikon gudanar da aikin ‘yan sanda a faɗin ƙasar nan, kuma gwamnatin tarayya ce ke kula da ita.

Sai dai ƙaruwar matsalolin tsaro kamar ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci sun ƙara jawo kiraye-kirayen sauya tsarin domin bai wa jihohi damar kafa nasu rundunonin ‘yan sanda.

Domin wannan ƙudiri ya zama doka, dole ne ya samu goyon bayan aƙalla kashi biyu bisa uku na mambobin Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, sannan kuma a samu amincewar aƙalla majalisun dokokin jihohi 24 daga cikin jihohi 36 na ƙasar nan.

By ukarofi

Leave a Reply