Ministan Tsaro ya musanta jita-jitar murabus yayin da ya gana da Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ci alwashin ɗaukar matakin shari’a akan waɗanda suke yaɗa rahotannin da ke zargin cewa ya yi murabus daga muƙaminsa, inda ya ce hakan ya matuƙar girgiza shi kuma bai san daga ina aka samo zancen ba.

Janar Musa ya bayyana haka ne jim-kaɗan bayan wata ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ministan ya isa fadar ne da misalin ƙarfe 3 na yamma kuma ya tafi bayan sa’a guda yayin da ake raɗe-raɗin makomarsa a kujerar muƙamin ministan tsaron.

Da yake ganawa da manema labarai, Christopher Musa ya yi watsi da iƙirarin cewa ya yi murabus, inda ya tirje akan cewa babu wata magana mai kama da haka daga ɓangarensa, yana mai cewa wasu mutanen da ba su gamsu da ci-gaban da ake samu ba ne a harkar tsaro suke yaɗa batun.

Ya bayyana cewa, za su ɗauki matakin shari’a akan dukkan wanda aka gano yana da hannu a iƙirarin yayin da bincike ya yi fallasa.

A cewarsa, an ƙirƙiri jita-jitar ne da nufin rushe ƙwarin-gwiwar al’umma akan ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na warware matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya.

Har ila yau, ya ce sun gana da Shugaba Tinubu akan ba’asin al’amuran tsaro, wanda shugaban ƙasar ya nuna gamsuwa akan ƙoƙarin dakarun tsaron Nijeriya.

Kazalika, ya roƙi al’umma da su cigaba da bada goyon bayansu da haɗin kai ga jami’an tsaro yayin da suke ƙoƙarin shawo kan matsalar taɓarɓarewar tsaro a yankunansu.

By Babaji

Leave a Reply