Tinubu ya karɓi Sanata Hanga da Sanata Gaya yayin da suka koma APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Lahadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin Maitaimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanatan Barau Jibrin, Sanata Rufa’i Hanga da kuma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ya gana da manyan ‘yan siyasar ne yayin shirin tarbar Sanata Hanga da Sanata Kabir Gaya wajen komawa cikin jam’iyyar APC, lamarin da ke nuna ƙarin ƙarfi ga jam’iyyar mai mulki yayin tunkarar zaɓen 2027.

A yayin ganawar, Tinubu ya yi maraba da sanatoci biyun zuwa cikin APC, inda ya kuma jinjina wa matakin nasu na haɗewa da jam’iyyar domin kai ta ga nasara a babban zaɓen da ke tafe.

Haka kuma, ya bayyana dawowar tasu a matsayin babbar nasara da za ta bunƙasa haɗin kai da fahimtar juna da kuma nasarar siyasa a Jihar Kano da kuma sauran sassa Nijeriya, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa matsayin jam’iyyar a fannin siyasa.

Sanata Barau, Hanga da Gaya a nasu ɓangaren, su ma sun jaddada ƙoƙarinsu na bayar da cikakken goyon baya ga shirin Shugaba Tinubu na Sabunta Fata.

Kazalika, sun ƙudiri aniyar cigaba da tallafa wa tsare-tsare da shirye-shiryen Tinubu domin tabbatar da sun cimma nasarori da kuma ci-gaban Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply