(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
Funke Adekoya (SAN) ta yi takara sau biyu, a shekarun 2006 da 2014, amma ba ta yi nasara ba. Foluke Dada-Lawanson ma ta shiga tseren 2026 kafin daga bisani ta janye bayan cimma matsayar bai ɗaya da aka yi a yankin Yammacin ƙasar.
Saboda haka, lokacin da Oyinkansola ta sanar da cewa ita ma za ta shiga takara, mutane da dama ba wai suna kallon zaɓen na zaɓar shugaba kawai ba. Suna kallon ko tarihi zai sake bai wa mace damar zama shugabar ƙungiyar ta hanyar cikakken zaɓe a karon farko.
Tambayar ana. Ita ce, shin ya ta gudanar da yaƙin neman zaɓen?
Ta gudanar da yaƙin neman zaɓenta ƙarƙashin taken: “A Bolder Bar That Works for Eɓeryone.”
Taken ya ta’allaƙa ne kan inganta walwalar lauyoyi, ƙarfafa riƙon amana a cikin ƙungiyar da kuma rage tsadar gudanar da sana’ar lauya.
Kafin ranar kaɗa ƙuri’a, an samu muhawara da shari’o’i kan batun wanda ya kamata ya zama ɗan takarar bai ɗaya daga yankin Yamma. Daga baya kuma, wasu daga cikin abokan takararta sun nuna damuwa kan yadda aka gudanar da tsarin zaɓen.
ƙalubalen bai tsaya nan ba. A daidai lokacin da ake shirin buɗe tsarin kaɗa ƙuri’a ta intanet, Kwamitin Gudanar da Zaɓen NBA ya sanar da cewa dandalin zaɓen ya fuskanci harin masu kutse ta yanar gizo.
Wannan lamari ya tilasta jinkirta fara zaɓen tare da sauya tsarin zuwa wani sabon dandali da aka ƙara wa kariya.
Duk da wannan yanayi, zaɓen ya gudana cikin sa’o’i ashirin da huɗu. Tun daga farkon ƙidayar ƙuri’u, Oyinkansola ta ci gaba da jan ragamar sakamakon, kuma tazarar da ke tsakaninta da sauran ‘yan takara ta riƙa ƙaruwa a hankali.
Lokacin da aka kammala ƙidaya, ta samu ƙuri’u 12,317, waɗanda suka kai kashi 47.18 cikin ɗari na jimillar ƙuri’un da aka kaɗa.
Wannan sakamako ne da ya tabbatar da nasararta, tare da tabbatar da wani sabon tarihi da aka daɗe ana jira a cikin ƙungiyar Lauyoyin Najeriya.
A lokacin da aka bayyana sakamakon, saƙonnin taya murna suka fara mamaye kafafen sada zumunta da dandamalin lauyoyi.
Amma abin da ya fi ɗaukar hankali ba yawan saƙonnin ba ne, sai irin ma’anar da mutane suka ɗora wa wannan nasara.
Ga wasu, nasarar Oyinkansola ta kasance sakamakon gogewa da hidimar da ta shafe shekaru tana yi wa ƙungiyar. Ga wasu kuma, wata alama ce da ke nuna cewa NBA ta shiga wani sabon zamani da ake ƙara bai wa aiki da cancanta muhimmanci.
Ko da yake kasancewarta mace shi ne abin da ya fi jan hankali a kanun labarai, waɗanda suka yi aiki tare da ita sun fi karkata ga wata siffa dabam.
Sun bayyana ta a matsayin lauya mai sauraro, mai natsuwa wajen yanke hukunci, kuma mai son gina matsaya ta hanyar tattaunawa maimakon ɗora ra’ayi da ƙarfi.
Irin waɗannan halaye ne suka sa ta yi fice a fannin sasanci, inda ake buƙatar nutsuwa da hikimar haɗa ɓangarori masu saɓanin ra’ayi zuwa teburi guda.
Watakila saboda wannan gogewa ce ta sa ba ta gina yaƙin neman zaɓenta a kan kasancewarta mace kawai ba. Maimakon haka, ta fi karkata ga abin da ta yi imanin zai haɗa lauyoyi baki ɗaya; inganta walwalarsu, ƙarfafa riƙon amana a cikin ƙungiyar da kuma rage nauyin da tsadar gudanar da sana’ar lauya ke ɗorawa a kansu.
A lokuta daban-daban kafin zaɓen, ta yi nuni da cewa shugabanci ba ya samun karɓuwa ta hanyar kalamai masu armashi kaɗai. A cewarta, ƙungiya mai ƙarfi ita ce wadda kowane mamba yake jin yana da muhimmanci, kuma ake sauraron muryarsa ba tare da la’akari da matsayin da yake kai ba.
Wannan tunani ya yi daidai da irin tafiyar da ta yi cikin NBA. Ta fara daga ayyukan da ba su da ɗaukar hankali sosai, ta yi aiki a kwamitoci, ta shirya taruka, ta ba da gudunmawa wajen tsara manufofi, kafin daga bisani ta nemi jagorancin ƙungiyar.
Saboda haka, wasu masu lura da harkokin ƙungiyar suka bayyana nasararta a matsayin sakamakon doguwar tafiya, ba wani abin mamaki da ya faru cikin dare guda ba.
Sai dai, kamar yadda yake a kusan kowace babbar nasara, akwai darussan da suka zarce batun wanda ya lashe zaɓe.
Labarin Oyinkansola ya sake tunatar da cewa hanyar zuwa kololuwa ba koyaushe take zama madaidaiciya ba.
Ta fara ne da karatun Turanci, ta kuma ɗauki tsawon shekaru kafin ta koma makaranta domin nazarin shari’a, ta gina kanta a cikin sana’a mai tsauri, ta shiga gwamnati, ta koma zaman kanta, sannan ta shafe fiye da shekaru ashirin tana yi wa ƙungiyarta hidima kafin daga ƙarshe ta kai matsayin da ake gani a yau.
Akwai waɗanda kan ɗauki jinkiri a matsayin koma baya. Amma wasu lokuta, jinkiri shi ne ke bai wa mutum damar tara abin da zai sa ya tsaya da ƙafafunsa idan lokacin ɗaukar nauyi ya zo.
Tafiyar Oyinkansola na daga cikin misalan da ke nuna cewa ba tsawon lokacin da aka ɗauka ne ya fi muhimmanci ba; abin da aka yi da wannan lokacin ne yake ƙayyade inda mutum zai tsaya a ƙarshe.
A matsayinta ta shugabar NBA, nauyin da ke gabanta ya fi na kafa tarihi.
Domin lauyoyi na sa ran ganin yadda za ta fassara alkawuran da ta ɗauka zuwa manufofin da za su inganta rayuwar mambobin ƙungiyar, ƙarfafa martabar sana’ar lauya, da kuma ci gaba da kare ‘yancin kai na ƙungiyar a lokutan da ƙasa ke fuskantar muhawara kan doka, adalci da shugabanci.
Ko wane irin sakamako wannan sabon babi zai haifar a nan gaba?
Sunan Oyinkansola Badejo-Okusanya ya riga ya samu gurbi a cikin tarihin ƙungiyar Lauyoyin Najeriya. Ba wai kawai saboda ta zama mace ba, amma saboda ita ce mace ta farko da ta karya shingen da aka daɗe ana kallon ba zai rushe ba ta hanyar cikakken zaɓe.
Bari mu koma kan ɓangare mai muhimanci wato ko shugabar NBA tana da iyali?
Bayan dukkan matsayoyin da ta samu a fagen aiki da jagoranci, akwai wani ɓangare na rayuwarta da ba kasafai ake ganinsa a cikin manyan nasarori ba, wato rayuwarta a matsayin uwa, mata da kuma mace mai ɗauke da ragamar iyali.
Oyinkansola Badejo-Okusanya ta yi aure da Yomi Badejo-Okusanya, kuma Allah ya albarkace su da ɗa.
A bayan manyan ayyuka, tarurruka da nauyin jagoranci da take ɗauka, ta kuma kasance mace mai kiyaye mutunci darajar aurenta. Kuma ta sanya lokacin da take tare da iyalinta a matsayin lokaci mai muhimanci da nutsuwa.
Waɗanda suka san ta sun bayyana cewa tana da sha’awar karatu, kiɗa da tafiye-tafiye; abubuwan da suka taimaka wajen faɗaɗa tunaninta da kuma ba ta damar kallon duniya daga fannoni daban-daban.
Har ila yau, tana da alaƙa mai ƙarfi da addini, inda take aiki a matsayin mawaƙiya da kuma ma’aikaciyar coci a Emmanuel Chapel, Methodist Church Nigeria da ke Ikoyi, Legas.
Wannan ɓangare na rayuwarta yana nuna yadda ta haɗa ƙwarewar sana’a da kuma ƙimar da ta gada daga tarbiyya.
Domin a wasu lokuta, nasarar mutum ba ta tsaya ga kujerar da ya zauna ba ko taken da aka ɗora masa. Tana kuma bayyana ne ta hanyar halayen da yake nunawa a rayuwar yau da kullum, yadda yake mu’amala da mutane da kuma irin tasirin da yake bari ga waɗanda suka zo bayansa.
Labarin Oyinkansola Badejo-Okusanya ba kawai labarin wata lauya ce da ta zama shugabar wata babbar ƙungiya ba.
Labarinta na ɗauke da darasi ga duk wanda yake da buri amma yake ganin hanya ta yi tsawo, ko kuma yake ganin wasu ƙofofi sun daɗe a rufe.
Domin a rayuwa, wasu ƙofofi ba a buɗe su da gudu ko hanzari. Ana buɗe su ne da shekaru na shiri, da juriyar tsayawa a hanya, da kuma amincewa cewa aikin da ake yi a ɓoye wata rana zai samu damar bayyana kansa.
Bayan shekaru 34 ana jira, wata mace ta zo ta rubuta sabon shafi a tarihin ƙungiyar Lauyoyin Najeriya. Amma abin da ya fi muhimmanci ba wai kawai kujerar da ta samu ba ce; shi ne tafiyar da ta yi kafin ta isa wurin.
Tafiya ce da ta nuna cewa shugabanci ba kyautar lokaci ba ne; ana gina shi ne. Ba a fara shi ba a ranar da aka ɗaga hannu ana rantsar da mutum ba. Yana farawa ne tun lokacin da mutum ya zaɓi yin aiki cikin gaskiya, ya tara ilimi, ya gina mutunci, ya yi hidima ba tare da gajiya ba.
A cikin tafiyar Oyinkansola Badejo-Okusanya akwai darasin da ya wuce batun zama mace ta farko da ta kai wannan matsayi.
Darasin shi ne yadda mutum zai iya gina tarihi ba tare da ya ɗaga murya yana neman a gan shi ba.
Shekaru da dama da ta shafe tana aiki a bayan fage sun nuna cewa ba kowace nasara ce take zuwa da ƙararrawa ba. Wasu nasarori suna girma ne a hankali, kamar itacen da aka dasa a yau amma sai bayan shekaru aka ga inuwarsa.
Ta fara ne a matsayin ɗalibar Turanci mai burin neman ilimi. Daga baya ta koma fannin shari’a, ta fuskanci sabbin ƙalubale, ta gina kanta a cikin sana’a mai tsauri, ta shiga gwamnati, ta koma zaman kanta, sannan ta yi shekaru tana ba da gudunmawa ga ƙungiyar da daga baya za ta jagoranta.
A kowane mataki, akwai abubuwan da suka haɗa tafiyarta wuri guda; haƙuri, aiki tuƙuru da kuma amincewa cewa abin da ake ginawa da gaskiya ba ya ɓacewa.
Domin a rayuwa, wasu mutane suna neman kujera kafin su shirya nauyin da ke kanta. Wasu kuma suna shafe shekaru suna shirya kansu, har zuwa lokacin da kujera ta zo ta same su a shirye.
Oyinkansola Badejo-Okusanya ta kasance cikin rukuni na biyu. Saboda haka, tarihinta ba zai tsaya kawai a kan cewa ita ce mace ta farko da aka zaɓa kai tsaye domin shugabancin NBA ba.
Tarihinta zai kuma kasance tunatarwa ga waɗanda ke ganin jinkiri tamkar rashin nasara ne, ko kuma waɗanda ke tunanin aikin da ake yi a ɓoye ba shi da tasiri a gaba.
Wani lokaci, lokaci ba ya hana mutum isa inda yake son zuwa. Yana shirya shi ne domin idan ya isa, ya isa da abin da zai ba shi damar tsayawa.
A wannan makon, shafin Gimbiya ya kawo ƙarshen labarin Oyinkansola Badejo-Okusanya; matar da ta nuna cewa manyan canje-canje ba sa samuwa saboda kawai mutum ya nemi a ba shi dama.
Suna samuwa ne idan mutum ya shafe shekaru yana shirya kansa domin lokacin da damar zata zo.
Domin rayuwa na koyar da mu cewa, ba kowane mai jira ne yake ɓata lokaci ba. Wasu suna jira ne yayin da suke gina abin da zai sa duniya ta tuna da su.
