Sanata Rufa’i Hanga ya fice daga NDC a hukumance

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Rufa’i Hanga, ya yi fice daga jam’iyyar NDC a hukumance, lamarin da ya kawo ƙarshen tarayyarsa da ita a nan take.

Rahotanni sun nuna cewa, Sanata Hanga, wanda shi kaɗai ne sanatan NDC daga arewacin Nijeriya kuma mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye majalisar, ya sanar da murabus ɗin nasa ne a wata takarda da ke ɗauke da 3 ga Agusta, 2026, kuma ya gabatar da ita ga shugaban jam’iyyar na Gundumar Najeria da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa.

Ɗan Majalisar ya ce, ya ɗauki matakin ne bayan nazari bisa tsanake da kuma raɗin kansa, yana mai cewa hakan zai fara aiki ne a nan take.

Hanga ya kuma miƙa godiyarsa ga kwamitin zartarwar jam’iyyar na gundumar tasa da mambobin jam’iyyar bisa goyon baya da haɗin kai da ya samu a lokacin kasancewarsa a NDC.

Saidai, sanatan bai bayyana matakinsa na gaba ba a harkar siyasa ko nuna ga jam’iyyar da yake son komawa, amma ana jita-jitar akwai yiwuwar ya koma jam’iyya mai mulki (APC) yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.

Wannan mataki ya nuna cewa a yanzu NDC ba ta da wakilci a majalisar dattawa daga arewacin Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply