Sautin Shehu ya taka inda ƙafarsa ba ta taka ba!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Sautin Musulunci ya taimaki Shehu Mujaddadi ya kafa daula ba gidan rediyo, talaibijin ko soshiyal midiya ba. Shehu ba ya riƙe takobi ko mashi amma kullum hannunsa rike ya ke da alƙalami da tawada don yaɗa ilimi

Idan mu ka duba rayuwar Shehu Mujaddadi daga 1754-1817 ba kafafe na sadarwa ko ɗaya balle a je ga maganar wayar tarho don sai bayan shekara kimanin 70 bayan rasuwar Shehu a shekarun 1880’s a ka ma fara aiki da sadarwar TELEGRAPH a Nijeriya da kan fidda saƙo na layi 100 a wasiƙance kuma har 1920 da ƙaddamar da sadarwa a Lagos akwai layuka 920 na tarho a dukkan Nijeriya. Yau kowa a maha’inta a ramin ƙurar da ya ke boye na Zallawa, ya na riƙe da salula da ya duƙufa ga ingiza Musulmi su shiga ɗauki ba daɗi da juna.

A nan mahaifarsa ƙasar Gobir, Shehu ya zauna ya cigaba da karantarwa har Allah ya yi ma sa rasuwa don haka, yaya a ka yi jama’a su ka ji labarinsa daga dukkan yankunan Arewa na yanzu har da makwabta kuma su ka yi mubaya’a? Wallahi wannan aikin daga Allah ne da kan taimaki duk wanda ya tsaya kan tauhidi. Hatta sufuri sai ta kan dawaki, jakuna da ma taka sayyada a loakcin, duk da haka bai hana masu imani zuwa wajen Shehu don karo ilimi da neman addu’a ba. Duk nasarar ta Shehu ta biyo bayan addu’a da ya kan yi wa jama’arsa ta alheri ne in za su koma gida ko yankunan da za su tafi don da’awa.

Sarakunan zamanin Shehu na rike da makamai da mallakar dakaru masu shafe fuskarsu da shuni su na mazurai yayin da Shehu ke riƙe da alkalami da tawada amma duk ya rinjaye su. Hatta a yakin da Shehu ya yi na kare kai daga farmakin Sarki Yunfa, ba da ƙarfin makami ya yi nasara ba, amma da ƙarfin imani!.

Shehu bai rike wayar salula ba amma yau duk wayoyin salula na masoya da makiya na cike da bayanai na gaskiya da akasin haka kan rayuwarsa da dududu shekaru 63 ya yi a doron duniya ya rubuta littattafai da har abada za a cigaba da cin moriyarsu. Zan sake maimaitawa Shehu iya ƙasar Gobir kafarsa ta taka, bai taba zuwa Katsina, Kano ko Zazzau ba amma muryarsa da ikon Allah ta je birane da ƙauyukan da a ka ƙarfafa addinin tauhidi.

Sarki Yunfa ya yi yunƙurin bindige Shehu don kowa ya huta da wa’azi amma albarushinsa ya koma kansa. Wallahi ba dabarar Shehu ba ce, Allah ne ya taimake shi da karama don ikilasinsa

Da yawa masu aibata Shehu Mujaddadi ba sa kawo asalin tarihn yadda Sarkin Gobir Yunfa ya gayyato Shehu ya kuma zaro bindigarsa ya buɗewa Shehu wuta da albarusai amma makircin ya juya kansa. Maimakon Yunfa wanda almajirin Shehu ne ya karawa Shehu ƙarfi don bunƙasa koyarwar Musulunci, sai ya ga sarautarsa ba za ta yi yadda ya ke so ba, matuƙar ya bar addinin Musulunci ya yi karfi har mutane su ka waye da sanin dokokin Allah, su na gaba da na Sarki. Wata cin amanar ma ta hada da Shehu ne ma ya taimaki Yunfa ya zama Sarki a 1801 don masu neman sarautar su na da yawa a lokacin bayan rasuwar Sarki Nafata. Yo Shehu da ya yi rayuwa lami lafiya da Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo.

Bayan tsallake kisan gilla na Yunfa, Shehu ya koma garinsa Degel inda shi kuma Yunfa ke hana duk masu son zuwa wajen Shehu hurumin tafiya. A 1803, Yunfa ya kama wasu Musulmi a Gimbana don kawo su Alkalawa amma sai Shehu ya ɗau matakin ceto su yayin da a ka zo wucewa da su ta yankinsa. Wannan ya sa Yunfa ɗaukar alwashin wargaza Degel gaba ɗaya. Shehu ya ga bai dace ya shiga arangama da Yunfa ba don haka ya bar Degel ya yi hijira zuwa Gudu.

A 1804 Yunfa bai haƙura ba da niyyar murƙushe Shehu, sai ya nemi gudunmawar karin dakaru daga masarutu da ke makwabtaka don murƙushe Shehu inda a ka shata daga a yakin Tsuntsua, nan su Yunfa su ka kashe kimanin almajiran Shehu 2000 kuma cikinsu 200 mahaddata Alkur’ani ne!. Yunfa ya karanta Alkur’ani amma ba ya amfani da karatun, ya fi son shagalin duniya da more sarauta ba tare da takurar addini ba.

Allah mai yadda ya so Shehu ya samu tattara sauran mutanensa ya fito don kare kansa daga tsangwamar kisa ta Yunfa inda a 1808 ya yi nasara kan Yunfa a Alkalawa. Daga wannan lokaci malamai da sauran masu ƙaunar Musulunci su ka riƙa jin labarin Shehu don haka su ka je, ya koyar da su da yi mu su addu’a su koma garuruwansu don kafa tsarin Musulunci.

Shehu bai taka ko ina ba waje da ƙasar Gobir don haka bai taɓa zuwa Katsina, Kano ko Zazzau ba. Shehu bai taɓa kowa ba sai mutum ɗaya tilo da ya buɗe ma sa wuta da libarbar ta zamanin karni na 19.

WAIWAYE- Sarki Bawa jangwarzo na Gobir ya tsinke da lamarin shehu Rahimahullah tun da ya ki karɓar tarin dukiya a taron liyafar malamai. Buƙatar Shehu ga Sarki ita ce ya samu hurumin wa’azi ba tsangwama

Fitaccen tarihin shahararren Sarkin Gobir mai bin musulunci Bawa Jangwarzo, ya nuna ya gayyaci wata gagarumar liyafa ga manyan malamai a ƙasar Gobir don nuna mu su dukiya irinta sarauta da kuma su kara mika wuya ga matakan sarauta na babbar masarautar Gobir.

Cikin waɗanda a ka gayyata akwai Shehu Danfodio wanda ya halarci taron da kaninsa Balaraben Sudan Sheikh Abdullahi Gwandu. Yayin liyafar ta karramawa inda kowa ya yi tsit da dimaucewa da kyautar goma ta arziki daga Sarki, sai Shehu ya miƙe ya ce ya na da magana. Kowa ya sha mamaki don ba a iya yi wa Sarki magana sai dai mutum ya yi godiya ya dukar da kai. Shehu ya ce ba sa buƙatar dukiya ko ta kwayar zarra daga Sarki amma su na da buƙatar samun dama ta yin wa’azi ba tare da tsangwama ba. Sarki ya yi mamaki da gaskiya kazalika da gudun duniya na Shehu, ya amince Shehu ya cigaba da yin wa’azinsa.

Daganan Shehu ya samu ‘yancin yada kalmar Allah ga mutane, ya zama su ma mutanen su na zuwa ɗaukar karatu wajen Shehu ba tare da shakka ba. Hakanan Shehu ya zauna lafiya da Bawa Jangwarzo har Allah ya yi wa Sarki rasuwa. ƙanin Bawa mai suna Yakubu ya hau sarauta kuma shi ma musulmi ne. Bayan Yakubu ya rasu sai Nafata wanda ba Musulmi ba ne ya samu sarauta kuma ya daɗe ya na fatar damar kashe Shehu. Allah bai ba shi nasara ba sai dansa Yunfa ne ya nemi cikawa maƙiya Musulunci buri wajen neman kashe Shehu don a huta da Musulunci a Gobir.

Kasancewar Shehu ya dogara ga Allah bisa neman iklasi, Allah ya daga muryar Shehu wanda manyan makamansa, tawada ne da alƙalami ba takobi da mashi ba.

Duk wanda ke zagin Shehu a zamanin nan, duk mabiya tuggun su Yunfa ne da ke son shagalin duniya ta hanyar ture tasirin Musulunci.

Shehu Mujaddadi ba shi da faɗa kamar ta Sarki sai tsangayar daukar karatu. Malamai ne su ka je wajen shehu daga sassan arewa da kewaye, su ka dawo gida ko sassa don jaddada Musulunci

Duk mai kawowa Shehu Mujaddadi ya kwace sarautar wani mai sarauta, gaba ɗaya bai ma fahimci rayuwar Shehu ba, don Shehu har ya koma ga Allah bai kafa Fada ta sarauta ba sai tsangaya da a kan zo ɗaukar karatu. Maimakon Fadawa da kan zauna a Fada don fadanci, Shehu almajirai ya ke da su da kan zauna da shi kusan dare da rana don karatu.

Ba ko mutum daya da Shehu ya gayyato daga ko ina don ya zo wajensa ya karɓi tuta ya kuma koma don kafa sarauta. Duk waɗanda a ke ganin sun koma su ka zama jagorori a garuruwansu, kan malantar addini su ka tafi ba sarauta ba. Na kawo mu ku misali a baya na garuruwan da wasu ke magana kan sarauta kamar Katsina inda Malam Ummarun Dallaje ya taso daga Dallaje a Katsina ya tafi wajen Shehu daga nan ya juyo gida don kafa tsangayar karatu da gusar da duk tsarin camfe-camfe, bori da masu bautar Doguwa da giza-gizai. Asalin Ummarun Dallaje Balarabe ne kuma Katsinawa sun san haka.

Kano ma da a ke batun wai an ture mahaddacin Alkur’ani Sarki Alwali a Burunburun, wallahi sam Shehu bai ma san Malam Sulaimanu ba sai lokacin da ya taso daga Kano daga zuriyar Mundubawa ya taho wajensa ya kara saita karatunsa, daga nan ya dawo gida don koyarwa. To Shehu da bai san Malam Sulamanu ba sai ta da’awar yada Musulunci balle Alwali da a ka ƙirƙiri labaru a na alakanta ma sa. Tabbas Malam Sulaimanu ya ga tsarin da a ke bi a tsohuwar Kano ya keta dokokin Islama shi ya sa ya zo don tajdidi.

Ko Malam Musa na Zazzau wanda shi ma ɗan gida ne mutumin Zazzau ne na asalin-asali kuma malami ya tashi daga Zakzak ya tafi wajen Shehu don zama almajirinsa kuma ya dawo gida don kafa babbar makarantar yaƙar gargajiya ta zamanin duhun kai.

KAMMALAWA

Don haka in mun duba ba inda Shehu ya taka a garuruwan da a ke magana amma ƙaninsa Abdullahi Gwandu ya taba niyyar zuwa hajji inda ya biyo ta Kano, nan ɗalibai su ka tsayar da shi su ka yi ta kwasar karatu cikin salka-salka amma na ilimi har ya rubuta littafi a birnin KIFAYAT DUAFA’ASSUDAN FI BAYANI TAFSIRIL ALKUR’AN. Daga nan ma bai wuce ba sai ya juyo gida don cigaba da taya Shehu karantarwa.

Sam Shehu bai taɓa amsa sunan Sultan ko Sarki ba, matsayinsa shi ne jagoran addini wato AMIRAL MUMININ.

By ukarofi

Leave a Reply